Ko Liverpool za ta kado Arsenal a kan teburin Premier?

An wallafa

Liverpool za ta je gidan Fulham domin buga wasan mako na 34 a Premier League ranar Lahadi a Craven Cottage.

Liverpool tana mataki na uku a teburin kakar nan da maki 71, yayin da Manchester City ce ta biyu da maki 73 da kuma Arsenal ta daya da maki 74.

Ranar Asabar Manchester City ta kai karawar karshe a FA Cup, bayan da ta doke Chelsea 1-0 a Wembley.

Bayanan koshin lafiyar 'yan wasan:

Kociyan Fulham, Marco Silva bai da wasu sabbin 'yan wasan da suka ji rauni, watakila ya bayyana wadanda suka doke West Ham, domin fuskantar Liverpool.

Watakila kyaftin, Tom Cairney ya maye gurbin Sasa Lukic a gurbin tsakiya.

Haka kuma watakila dan wasan Liverpool, Trent Alexander-Arnold a fara wasan da shi a karon farko a Premier League, bayan sama da wata daya, domin maye gurbin Conor Bradley.

Joe Gomez na daf da komawa fagen daga, yayin da Thiago Alcantara da Joel Matip ke jinya.

Karawa tsakanin kungiyoyin biyu:

Liverpool ba ta yi rashin nasara ba a wasa biyar a Premier League a Craven Cottage ba, wadda ta yi nasara uku da canjaras daya.

Wasa daya Fulham ta yi nasara a karawa 13 baya da ta fuskanci Liverpool a dukkan fafatawa da canjaras uku da rashin nasara tara.

Fulham

Fulham ta yi nasara daya daga wasa hudu baya a Premier League da yin canjaras daya aka doke ta fafatawa biyu.

Fulham ta ci wasa tara daga 16 da ta yi a gida a Premier League, kwazo mai kyau tun bayan da ta koma buga babbar gasar tamaula ta Ingila a Cottage a 2011/12 da ta yi nasara 10.

Watakila kungiyar da Marco Silva ke jan ragama ta yi rashin nasara biyu a jere a gida a karon farko a kakar nan.

An zura mata kwallo 13 a wasa 15 baya a Premier League a Craven Cottage da yin wasa shida ba tare da kwallon ya shiga ragarta ba.

Liverpool

Liverpool ta yi nasara biyar daga wasa shida a waje a dukkan fafatawa da canjaras daya da rashin nasara daya.

Kungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama ta ci wasa shida daga 18 baya a Premier League a wasan hamayya a Landan da canjaras bakwai da rashin nasara biyar.

Liverpool ta zura kwallo a raga a wasa 19 a jere a waje, karo na biyu bayan cin kwallo a wasa 21 tsakanin Fabrairun 1955 zuwa Fabrairun 1956.

Mohamed Salah na fatan cin kwallo karo na uku a jere a Premier League a waje a karon farko tun bayan biyar da ya ci daga Agusta zuwa Oktoban 2021.