Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nawa ce darajar ƴan Man United da aka sa a kasuwa a bana?
Manchester United ta saka dukkan ƴan wasanta a kasuwa, bayan da take fatan hada kudin da za ta bunkasa kungiyar karkashin Ineos daga badi.
United ta kashe £1bn a shekaru da yawa wajen sayen ƴan wasan dake buga mata tamaula, amma ta kasa taka rawar gani a kaka da yawa har da karkashin Erik ten Hag.
Wannan ce kaka ta biyu da Ten Hag ya ja ragamar United, wanda ya dauki Carabao Cup a bara da samun gurbin Champions League a bara.
To sai dai a bana an yi waje da kungiyar Old Trafford daga gasar zakatun Turai cikin rukuni, sannan aka fitar da ita a Carabao Cup, bayan rashin nasara a hannun Newcastle.
Da yake kungiyar ba za ta samu gurbin shiga Champions League a badi ba, ya zama wajibi ta rabu da wasu ƴan kwallon a bana, domin ta samu gudanar da kungiyar kan cin riba.
Albashin da United kan biya ƴan wasanta ya kai £331m, kuma matsakaicin dan wasa da ake biya duk mako shi ne £154,000.
Kuma United ce ta hudu a biyan albashi mai tsoka tsakanin kungioyoyin Premier League, idan ka cire Manchester City da Chelsea da kuma Liverpool.
United tana ta shida a teburin Premier League da maki 54, bayan cin wasa 16 aka doke ta 12 da canajaras shida.
Kungiyar ta ci kwallo 52 a Premier League a kakar nan, aka zura mata 51 a raga a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Ranar Litinin 6 ga watan Mayu Crystal Palace za ta karbi bakuncin United a wasan mako na 36 a Premier League.