Ronaldo zai girbi abin da ya shuka - Ten Hag

Asalin hoton, Reuters
Erik ten Hag ya ce Cristiano Ronaldo zai girbi abin da ya shuka, bayan da ya tabbar dan kwallon bai yadda ya shiga ya yi canji ba a wasa da Tottenham.
Manchester United ta doke Tottenham 2-0 a gasar Premier League karawar mako na 12 ranar Laraba.
Ronaldo, mai shekara 37 ya bar Old Trafford tun kan tashi daga karawar, wanda ya tashi daga bencin da yake zaune a minti na 89 ya fice daga filin.
An cire sunansa daga 'yan wasan United da za su kara da Chelsea a Stamford Bridge ranar Asabar a babbar gasar tamaula ta Ingila, kuma shi kadai yake yin atisaye.
An tambayi Ten Hag ko Ronaldo ya ki yadda ya canji dan wasa - sai Ten Hag ya ce ''gaskiya ne.''
Ya kara da cewar karo na biyu kenan yana wannan halayyar, domin ya yi haka a wasan sada zumunta da Rayo Vallecano - saboda haka dole ya fuskanci hukunci.
''Tattaunawa ce tsakani na da Cristiano. Dukkan bayanai a fayyace suke, a bayanan yana cikin fitattun 'yan wasan kungiyar, ''in ji Ten Hag.
''Nine kociya, alhakin da'a na karkashi na. Dole na yi nuni da doka da oda da nake rike da ragama, zan kuma tauna tsakuwa. Mu kungiya ce, ya kamata kanmu a hade.
''Bayan wasa da Rayo Vallecano na fada cewar ba za nu amince da halin rashin da'a ba, ba kawai a kansa ba a gabaki dayan kungiyar, tun da ya kara aikata laifin zai girbi abin da ya shuka. Abin da zai faru kenan za mu hukunta shi.
An caccaki Ronaldo kan halin da ya nuna ranar Laraba, tun daga masu sharhin wasanni da magoya bayan kungiyar da masu ruwa da tsaki a harkar tamaula.
Ronaldo ya ci kwallo daya a wasa takwas a Premier Leagu a bana, wanda ya nuna bai ji dadi ba da aka sauya shi a wasa da Newcastle ta tashi 0-0 da United a gasar Premier.
United za ta je Stamford Bridge a mataki na biyar a kan teburi da tazarar maki daya tsakaninta da Chelsea ta hudu ranar Asabar, Ten Hag ya ce baya fatan batun Ronaldo ya janye hankalin 'yan wasa kan kalubalen da ke gabansu.










