Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsaloli biyar da BBC ke fuskanta yayin da ta cika shekara 100
Ƙalubale biyar da BBC ke fuskanta yayin da ta cika shekara 100 da kafuwa
Yayin da kafar yaɗa labaru ta BBC ke bukin cika shekara 100 da kafuwa, aya daga cikin editocin BBC ya hango gaba, kan irin alubalen da BBC ke fuskanta, tun daga gogayyar da za ta yi da masu yaɗa shiri kai-tsaye zuwa yadda za ta janyo hankalin matasa a TikTok.
Lokacin da Lord Reith - ya zama shugaban BBC na farko, ya zo a matsayin ɗan kishin ƙasa. Masanin ƙere-ƙeren ɗan asalin Scotland ya zo da tunanin kawo ci gaba na zamani domin sake gina ƙasar, wadda yaƙi ya yi wa matuƙar illa.
Inda a wannan zamanin ne, mutane kaɗan ne za su yi tunanin a samar da kafar yaɗa labaru. Kuma mutane kaɗan ne za su yi tunanin a rinƙa samar wa kafar kuɗeɗe kai-tsaye daga abin da al'umma za su rinƙa biya.
Amma idan aka yi la'akari da aikin da BBC ta yi lokacin bikin bizine sarauniyar Ingila, za a ga cewa lallai BBC ta kasance kafar yaɗa labaru ta ƙwarai a faɗin duniya.
A tsawon shekara 100, BBC ta kasance tare da mutanen Birtaniya a kowane lokaci na muhimman abubuwan da ke faruwa a cikin gida ko kuma waje.
Kamar lokacin da Churchill ya gabatar da jawabinsa na yaƙin duniya, da naɗin sarautar sarauniya, da gasar cin kofin duniya na 1966, da dai sauran su.
Yawancin al'ummar Birtaniya sun samu waɗannan labarai ne daga BBC. To amma yanzu haɗa al'ummar ƙasar wuri guda ya zama babban ƙalubale saboda yadda ƙasar ta sauya, da kuma yadda harkar yaɗa labaru ta sauya.
A tsawon waɗannan shekaru 100, BBC ta rinƙa amfani da kayan aiki na zamani domin faranta ran al'umma.
An kafa BBC ne a lokacin da rediyo ke tashe, daga nan ta fara kawo shirye-shiryen talabijin.
Samun sauye-sauye a ɓangaren kayan aiki na zamani - da fitowar yanar-gizo, da shafukan sada zumunta, da wayoyin hannu na zamani sun raunana al'adar mutane ta dogaro da BBC wurin samun bayanai.
Waɗannan sauye-sauye su ne tushen irin ƙalubalen da BBC ke fuskanta a wannan zamani. Ga biyar daga cikin ƙalubalen...
Yarda
Ya na da matuƙar wahala kafin mutane su amince da mutum, amma abu ne mai sauƙi wannan yardar ta kau.
Faruwar badaƙala a-kai a-kai - kamar abin da ya faru na tonon silili game da ma'aikacin BBC Jimmy Savile, wanda bayan rasuwar sa aka gano cewa ya rinka lalata da yara, da tattaunawar ma'aikacin BBC Martin Bashir da gimbiya Diana, inda aka zarge shi da yaudara domin ya samu damar yin tattaunawar - da wasu abubuwa da dama da suka faru - sun sanya yardar da mutane suka yi da kafar ta BBC ta ragu.
Yanzu ana cikin wani zamani ne na yawaitar labarun ƙarya. An daina bai wa sahihan labarai muhimmanci kasancewar labaran ƙarya sun fi saurin yaɗuwa. Shafukan sada zumunta sun yi mummunar illa ga harkar yaɗa labaru.
Wannan babbar dama ce ga ƴan jarida waɗanda ke kashe dukiya da lokacinsu wurin zaƙulo gaskiya, kamar yadda mafi yawan mutane za su so.
To amma rashin yarda da mutane ke nuna wa BBC babbar illa ce. Mutane ba za su kashe kuɗinsu a kan abin da ba su yarda da shi ba.
Kuɗi
Dole ne BBC ta ji jiki kasancewar tana gogayya ne da manyan kamfanoni masu arziƙi kamar Netflix da Disney.
BBC tana samun kuɗi kimanin fan biliyan biyar. Kuma ana sanya mata ido sosai a kan yadda take kashe kuɗi, sannan tana fuskantar matsi daga ƴan siyasa.
Yaɗa shirye-shirye kai-tsaye ta intanet ya sanya kuɗin da ake kashewa wajen haɗa shirye-shirye sun yi tashin gwauron zabi.
Hakan na nufi dole BBC ta taƙaita irin wannan tsari, kuma hakan na nufin dole BBC to samo dubarun yin abin da wasu ba za su iya yi ba.
Tafiya da matasa
Akwai matuƙar banbanci kan irin labaran da mutane ke so daga BBC.
Matasan Birtaniya da ke tsakanin shekaru 16 zuwa 24 sun fi ɓata lokaci suna kallon bidiyoyi a TikTok, a kan kallon talabijin.
A cikin shekara goma da suka wuce lokacin da matasa ke kashewa wajen kallon talabijin ya ragu da kashi biyu cikin uku.
Babbar matsalar da BBC ke tsoro ita ce rashin muhimmanci a tsakanin al'umma. Saboda haka dole ne BBC ta tabbatar tana da muhimmanci tsakanin al'umma, kuma ya zuwa yanzu tana da shi.
To amma manyan abubuwan da za su iya sanadin raguwar muhimmanci BBC tsakanin al'umma su ne bidiyoyin TikTok, da Netflix, da kuma Spotify.
Karɓuwa a wurin kowa
Wani abin mai alaƙa kuma shi ne yadda za ta karɓu a wurin kowa.
Idan har BBC na son ta ci gaba da samun kuɗi daga harajin da al'umma ke biya to dole ne ta samu karɓuwa a wajen kowa - ko kuma aƙalla a wurin akasarin al'umma.
Wannan ne ya sanya shugabanta Tim Davie ya fifita dawo da aidar BBC ta rashin nuna banbanci.
A ƙasa kamar Birtaniya, wadda al'ummarta suka waye, ga yawan banbance-banbance da saɓanin ra'ayoyi, samun karɓuwa a wurin kowa da kowa abu ne mai matukar wahala.
Duk da cewa BBC ta amince cewar dole ne ta rage yawan shirye-shiryenta, ta kuma mayar da hankali kan yin abubuwan da wasu ba za su iya yi ba, amma hanyar da take samun kuɗi a yanzu ta dogara ne a kan yadda za ta samu karɓuwa tsakanin kowane ɓangare na al'umma.
A kodayaushe BBC takan harzuƙa gwamnatoci. A yanzu akwai abubuwa guda biyu.
Na farko shi ne, a yanzu matsin da ake samu daga gwamnati ta fi yawa, duk da cewa akwai hanyoyin sada zumunta.
Na biyu shi ne, maƙiyan BBC za su iya kafa hujja da sabbin kafofin isar da labarai, domin nuna cewar babu hujjar ci gaba da karar harajin kallon talabijin daga al'umma.
Wasu za su ce hakan bai dace ba a wannan zamani na YouTube da Instagram.
Waɗannan matsaloli manyan ƙalubale ne ga ci gaban wanzuwar BBC.
Ba kowa ne zai yarda cewa tsarin da BBC ke samun kuɗinta zai iya ɗorewa zuwa wani lokaci mai tsawo ba nan gaba.
Amma kamar yadda aka gani a baya-bayan nan, har yanzu BBC na da mutunci a idon al'umma kuma tana nuna ƙwarewa a ayyukanta. Shugabancin kafar yaɗa labarun na da nasu tsare-tsaren na shawo kan matsalolin.
Dole ne BBC ta yi tafiya da zamani ta fannin aiki da kayan aiki matuƙar tana son mutane su ci gaba da bibiyanta, su ci gaba da biyan kuɗin kallon ta, kuma ta sha gaban abokan hamayya.
Babban fatan BBC bayan shafe ƙarni guda shi ne ta koma kan hangen nesan wanda ya kafa ta. Kamar yadda ya tabbatar a shekarar 1922, cewar babban ginshiƙin ci gaban BBC shi ne samar da shirye-shirye masu inganci, ba dole sai masu yawa ba.