Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Oxlade-Chamberlain na nazarin komawa Besiktas
Tsohon dan wasan Liverpool da Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain yana tunanin komawa kungiyar Besiktas ta Turkiyya.
Oxlade-Chamberlain, mai shekara 29, zai koma a kungiyar a kyauta bayan kwantiraginsa ya kare a Anfield a wannan bazarar kuma an yi masa tayin kwantiragin shekaru biyu tare da zabin kara na uku.
Sashen Wasanni na BBC ya fahimci cewa Oxlade-Chamberlain ya jawo hankalin kungiyoyi gasar Pro League ta kasar Saudiyya.
Oxlade-Chamberlain ya buga wasanni 146 kuma ya zura kwallaye 18 bayan ya koma Liverpool daga Arsenal akan kudi fam miliyan 35 a shekarar 2017.
Ya lashe gasar zakarun Turai da Premier tare da Liverpool kuma ya buga wa Ingila wasanni 35, inda wasansa na karshe ya kasance a shekarar 2019.