Ɗan wasan Stuttgart ya ƙi Man Utd, Arsenal na neman Zubimendi

An wallafa

Manchester United na nazarin zawarcin dan wasan gaba na Sevilla Youssef En-Nesyri, ɗan Moroko mai shekara 26, saboda ɗan wasan da take hari, Serhou Guirassy na Stuttgart mai shekara 27 na tawagar Guinea ya fi son tafiya Tottenham. (Sun)

Watakila Tottenham ta bai wa Chelsea ɗan wasan tsakiya na Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, a yarjejeniyar sayen Conor Gallagher na tawagar Ingila. (Sky Sports)

Aston Villa na son karɓar aron ɗan gaban Jamus Timo Werner daga RB Leipzig a ƙoƙarin da ƙungiyar mai tashe a Premier ke yi domin ƙarfafa gabanta. (Football Insider)

Chelsea ta tuntuɓi ƙungiyar Sporting Lisbon ta Portugal ko za ta sayar mata da ɗan bayanta na Ivory Coast Ousmane Diomande, mai shekara 20, da kuma ɗan gaban Sweden Viktor Gyokeres, a watan Janairu. (Evening Standard)

Arsenal na son ɗan wasan tsakiya na Real Sociedad Martin Zubimendi to amma ɗan tawagar Sifaniyar ba ya son sauya ƙungiya a watan Janairu. (Football.London)

Inter Milan na shirin gabatar da buƙatar aron ɗan wasan tsakiya na Celtic Matt O'Riley a watan Janairu tare da sharaɗin sayensa gaba ɗaya a ƙarshen kaka, to amma kuma Aston Villa da West Ham ma na matuƙar son ɗan wasan na tawagar Denmark, haihuwar Ingila. (Sky Sports)

Ɗan wasan tsakiya na Sunderland Pierre Ekwah, mai shekara 21, na ɗaukar hankalin Crystal Palace, da Fulham da Nottingham Forest, amma kuma ƙungiyar ba ta son rabuwa da ɗan Faransan saboda tana sa ran samun damar buga wasannin gasar Ingila ta Championship. (Evening Standard)

Luton Town na nazarin katse yarjejeniyar kaka ɗaya da ta kraɓi aron ɗan wasan Arsenal na tsakiya Albert Sambi Lokonga ɗan Belgium domin ƙarfafa wasu sassan ƙungiyar. (Teamtalk)

Har yanzu masu shirya gasar Super League ta Turai na da ƙwarin gwiwar shawo kan ƙungiyoyin Premier su amince da sabbin tsare-tsarensu duk da cewa ƙungiyoyin sun fito fili suna nesanta kansu daga gasar. (The i)

Everton na duba yuwuwar sayen ɗan wasan tsakiya na Burnley Josh Brownhill ɗan Ingila a watan Janairu. (Football Transfers)

Fulham ta cimma yarjejeniya da Fluminense ta sayen ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar ta Brazil Andre kuma yanzu ya rage da matasahin ɗan tawagar Brazil ɗin mai shekara 22 ya yanke shawarar ko yana son tafiya. (Football Insider)

Sevilla na duba yuwuwar aron ɗan wasan tsakiya na Bournemouth Hamed Traore, na Ivory Coast, a watan Janairu. (AS )