Rashin buga Champions League babbar dama ce gare mu - Pochettino

An wallafa

Mauricio Pochettino ya ce Chelsea ta yi amfani da rashin buga gasar Cin Kofin Zakarun Turai a wannan makon wajen shirya wa wasannin da ke gabanta a gasar Premier na wannan kakar.

Kungiyar ta Stamford Bridge ta kasa samun gurbin buga Champions League a karo na biyu a cikin shekaru 26 bayan ta kare a mataki na 12 a gasar Premier ta bara.

Sun yi nasara sau ɗaya a wasanni biyar na farko a kakar wasan bana inda ta ke a mataki na14.

Pochettino ya ce magoya bayan kungiyar na da damar nuna rashin gamsuwarsu bayan da suka tashi babu ci da Bournemouth a karshen makon da ya gabata, amma ya ce ya gamsu da rawar da kungiyar ta taka.

Chelsea za ta karɓi bokuncin Aston Villa a wasanta na gaba a ranar Asabar.