Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rauni zai hana Jesus fara gasar Firimiya ta bana
An yi wa dan wasan gaba na Arsenal, Gabriel Jesus karamar tiyata a gwiwarsa kuma ba zai buga wasannin farkon gasar Firimiya ta bana ba.
Jesus bai taka leda ba a wasan da suka doke Monaco a wasan sada zumunta da suka buga ranar Laraba ba kuma kocin kungiyar Mikel Arteta ya tabbatar da cewa dan wasan na Brazil zai yi jinya zuwa wasu makonni.
Raunin dan wasan mai shekaru 26 na da alaka da matsalar gwiwa da ya samu a kakar wasan da ta wuce, wanda kuma ya bukaci a yi masa tiyata.
Da yake magana bayan Arsenal ta yi nasara kan Monaco da ci 6-5 a bugun fenariti bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 a filin wasa na Emirates, kocin na Gunners ya ce Jesus ya fara jin zafi a gwiwarsa a makonnin da suka gabata.
Raunin dan wasan ya zo ne kwanaki hudu kafin Arsenal ta fafata da Manchester City a gasar Community Shield da kuma kwanaki 10 kafin wasansu na farko a gasar Premier da Nottingham Forest.