Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City za ta kara kujerun zaman 'yan kallo a Etihad
Manchester City ta mika takardun neman izinin fadada filin Eihad kan £300m.
City na son kara kujerun zaman 'yan kallon tamaula a Etihad daga 53,400 zuwa 60,000, wadda ke fatan fadada bangaren Arewacin filin.
Cikin kare-karen da za ta yi wa filin har da wurin shaye-shaye a saman ginin da gyara fasalin rufin filin wasan da shaguna da wajen adana kayan tarihi.
Ta kuma ce za ta gina otal da zai dauki gadon kwanan mutun 400 da sauran tsare-tsaren da ta gabatar ga hukuma don neman izini.
Kungiyar ta ce aikin da zai kai shekara uku ana yi kan a kammala, zai samar da yanayi na cudanyar magoya baya da samar da nishadi da walwala.
City ta ce shirin da take yi zai lashe kudi £300m zai kuma samar da aiki ga mutum 2,600, za kuma ta bayar da fifiko ga mutanen Greater Manchester.
Haka kuma za a gina ofisoshi don bai wa masu kasuwanci haya, wadanda za su bunkasa kungiyar ta hanyar hadin gwiwa.
Tun cikin watan Agusta City ta sanar cewar ta fara tattaunawa kan yadda za ta fafdada filin Etihad da wajen zaman 'yan kallon tamaula.
An gina Etihad a 2002 don karbar bakuncin Commonwealth Games daga nan ya koma wajen da Manchester City ke buga wasanninta a 2003.
A shekarar 2015 aka kara kujerun zaman 'yan kallo zuwa 6,000, kawo yanzu Etihad shine na biyar a jerin filin da ke cin 'yan kallo da yawa a Premier League.