Fina-finan ban-tsoro shida da aka haramta saboda razanarwarsu

An wallafa

Me zai faru idan fim ya kasance mai ban tsoro sosai? Ba abin da za a yi da ya wuce a karshe a haramta shi.

Duk da cewa fim din ban-tsoro zai iya kasancewa mai kyau da ban sha’awa, zai kuma iya kasancewa mai tayar da hankali.

Ga wasu daga cikin fina-finan ban-tsoro shida da aka haramta nuna su a talabijin.

Sai dai a sani cewa wannan rubutun yana ɗauke da wasu hotuna da za su iya tayar wa mutum hankali.

1) The Exorcist

Wannan fim ya kasance ɗaya daga cikin fitattu na ban-tsoro masu ɗaukar hankali da kusan kowa zai so ya kalla. Fim ɗin ya yi suna a duniya lokacin da aka fito da shi a 1973.

Wannan fim na wata yarinya da aljanu suka kama sannan batun yi mata ruƙiyya ya biyo baya ya ɗauki hankali tare da ƙayatar da masu sha’awar fim ɗin ban-tsoro a faɗin duniya.

A Amurka an rinƙa yin dogon layi cikin tsananin sanyi ga dusar ƙanƙara na zuba wajen shiga gidan sinima don kallon fim din.

Ƴan jarida sun rinƙa bayar da rahotannin mutane na suma wasu na amai ana fitar da su daga sinima lokacin kallon fim din.

Hukumar kula da fina-finai ta Amurka ta sanya fim din a matsayin wanda ba za a bar yara su je kallonsa ba sai da rakiyar manya. Wasu ƙasashen kuwa dokar ta yi tsanani ma, ba a yarda yara su je kallon ba.

Da farko a ƙasar Singapore ma hukumomi sun haramta fim din  saboda ya saɓa dokokinsu na mutunta addini.

Daga baya dai gwamnati ta ɗage haramcin amma da sharadi na waɗanda za su iya kallon sa ba kowa ba yaro da babba.

A makwafciyar ƙasar, Malaysia nan ma an haramta shi.

Hukumar da ke sa ido kan fina-finai ta Birtaniya (BBFC)  kusan ta fi ɗaukar tsauraran matakai a kan harkar fim fiye da yawancin takwarorinta na duniya a shekarun da suka gabata.

Matakin da ta ɗauka a kan fim din shi ne inda ta sanya shi a rukunin waɗanda ƴan sama da shekara 18 ke da damar kalla ba tare da an cire wasu fannoni ko jirkita shi ba.

Sai dai kuma duk da wannan mataki hukumar ta sauya matsayi a kan bidiyon fim din a 1984, inda aka hana sayar da bidiyon fim din a shaguna bayan shekara hudu. An haramta sayar da fim ɗin tsawon karin shekara 11, duk da cewa ana nuna shi lokaci zuwa lokaci a gidajen sinima.

A shekarar 1999, hukumar ta Birtaniya ta kawo ƙarshen haramcin, inda ta zartar cewa duk da kasancewar fim din (The Exorcist) yana da ƙarfi da karsashi, to amma tasirinsa ya ragu ba kamar a shekara 25 da ta wuce ba.

Duk da ce-ce-ku-cen da ke tattare da fim ɗin ya zama na farko a fina-finai masu ban-tsoro da aka zaɓa domin ba shi lambar yabo ta fim ɗin da ya fi kyawun hoto (Award for Best Picture).

2) Cannibal Holocaust

A wajen masana, wannan fim din na ban-tsoro na Italiya wanda aka yi a 1979, ya kasance ɗaya daga cikin fina-finan tsoro da suka yi fice da ƙaurin suna a duniya a shekarun 1980.

A cikin fim din ana kashe dabbobi da gaske da kuma tsananin tashin hankali na zahiri.

Wurin ya kunshi wani fanni ne na fim ɗin inda masu ceto ke ƙoƙarin gano masu aikin haɗa fim a ƙungurmin dajin Amazon.

A Italiya an zargi darektan fim din, Ruggero Deodato, da kisan kai bayan da aka daina ganin wasu daga cikin taurarin fim ɗin a bainar jama’a.

Daga nan ne ya gabatar da ɗaya daga cikin su a kotu aka gan shi a zahiri, sannan aka yi watsi da shari’ar.

Duk da haka an zarge shi da laifin gana azaba ga dabbobi, sannan kuma aka haramta  nuna fim din na Cannibal Holocaust a ƙasar ta Italiya  tsawon shekara uku.

Haka kuma an haramta fim ɗin a kusan garuruwa 40, tsawon wasu shekaru. Ƙasashen da suka haɗa da Australia da Norway da Birtaniya UK da kuma Ireland.

Hatta Amurka wadda aka san tana da sassauci a kan fina-finai da ake ce-ce-ku-ce a kansu fiye da wasu kasashe, ta haramta fim ɗin na Cannibal Holocaust tsawon shekara biyar bayan an fitar da fim din a 1980.

An sake janye fim ɗin daga gidajen sinima ƴan makonni a 1985.

Duk da tsawon wannan lokaci sai a shekarar 2005 aka fitar da fim ɗin a Amurka a hukumance.

3) Grotesque

Wannan fim ɗin na ban-tsoro na Japan an yi shi ne a 2009, inda yake nuna yadda wani likita mugu ya riƙa gana ma wasu matasan ma’aurata uƙuba.

Dillalan sayar da fim ɗin sun yi fatan za su samu takardar sheda ta fim ɗin guda 18.

Hukumar fina-finai ta Birtaniya ta haramta shi a ƙasar saboda tsabar cin zarafi na lalata.

Da cewa fim ne da zai koyar da abubuwa na mugunta da rashin tausayi da imani, kuma a kan haka ta ƙi bayar da takardar sheda ga fim ɗin tare da hana nuna shi a ƙasar.

Har yanzu wannan haramcin yana kan fim din a Birtaniya da Malaysia da kuma Philippines.

A Japan ƙasar da aka yi fim ɗin, da farko ba wani surutu ko ce-ce-ku-ce da ake yi a kansa sosai.

To amma bayan da Birtaniya ta haramta shi, sai wasu daga cikin masu sayar da shi suka janye shi daga shafukansu na intanet kuma aka saki fim ɗin ba tare da wani matsayi ba.

Fim ɗin ya samu takardar sheda a Finland da Faransa da Italiya da Sweden da Netherlands da kuma Amurka.

4) The Human Centipede II

Fim ɗin da ya fara fita daga wannan kamfanin shi ne wanda aka fitar a 2009.

Fim ne na ban-tsoro na ƙasar Holland, wanda a cikinsa ake nuna yadda wani likita ɗan ƙasar Jamus ya sace wasu ƴan yawon buɗe idanu uku sannan ya jarraba wata tiyata mai tayar da hankali.

Sai kuma fim na biyu da ya biyo bayan wannan wanda shi kuma an yi shi ne sakamakon wani da ya ga abin da wannan likita ya yi a fim ɗin na 2009, inda shi ma ya yi ƙoƙarin kwatanta abin da likitan ya yi amma ya zarta wancan din.

Darektan fin din, Tom Six, yana bugun ƙirji da cewa fim ɗin nashi shi ne mafi ban-tsoro da tayar da hankali a tarihin duniya.

Fim ɗin mai suna 'The Human Centipede II', ya gamu da tsauraran matakai na sanya ido a kansa faɗin duniya, inda a wani lokaci sai an fitar da wasu sassa daga cikinsa kafin a nuna.

Hukumar sanya ido kan fina-finai ta Birtaniya ta ki amincewa da shi a watan Yuni na 2011. To amma bayan da kamfanin da ke dillancinsa ya amince ya cire wasu sassa 32 a cikinsa, hukumar ta amince a sayar da faifan DVD ɗinsa.

Hatta shi kansa faifan DVD ɗin a 2012 hukumar tace fina-finai ta New Zealand ta ce bai dace ba.

Har yanzu na haramta fim ɗin a Ireland da maldives da kuma Philippines.

5) Texas Chain Saw Massacre

Wannan fim ɗin na 1974 da aka haramta shi tsawon shekaru da dama, yana ɗaya daga cikin fina-finai na farko masu ban-tsoro da suka yi ƙaurin suna.

An yi fim ɗin ne a kan labarin mutumin nan da ya hallaka mutane da dama Ed Gein, wanda ya yi amfani da sassan jikin mutanen da ya kashe ya ƙawata gidansa.

Hukumar kula da fina-finai ta Australia ta hana lasisin amincewa da fim ɗin 'The Texas Chain Saw Massacre' tsawon wani lokaci.

Haka ma ƙasashe da suka haɗa da Brazil da Chile da Finland da Faransa da Iceland da Ireland da Malaysia da Singapore da Sweden da Norway da New Zealand da kuma wasu sassan ƙasar Jamus an hana nuna shi zuwa wani lokaci.

6) The Evil Dead

Wannan fim ɗin Amurka ne na ban-tsoro da aka yi a 1981 wanda ya yi fice sosai a matsayin na ƙungiyar matsafa.

An gina fim ɗin ne a kan wasu ɗaliban kwaleji su biyar da suka je hutu daji inda suka zauna a wata bukka.

A wannan zama da suka yi ne suka samu wani kaset na sauti, wanda a bisa kuskure suka saki wasu shaiɗanun aljanu waɗanda suka rinƙa kashe daliban.

Fim ɗin ya janyo ce-ce-ku-ce lokacin da aka sake shi saboda yana nuna tsabagen rashin imani da zubar da jini.

An haramta shi a ƙasashen Iceland da Malaysia da Singapore da Birtaniya da Ireland da Chile, zuwa wani lokaci.

Daga baya yawancin ƙasashe sun bayar da damar nuna fim ɗin amma wanda aka cire wasu sassa a ciki.

Fim ɗin na The Evil Dead ya zama wata harka ta samar da kuɗi inda aka yi kashi biyu, wanda ainihin darektansa Sam Raimi ya rubuta.

An kuma yi fim na hudu, Evil Dead, a 2013. An kuma yi wasan bidiyo na fim ɗin da kuma littattafai na ban dariya ɗauke da labarin.