Waiwaye: Buhari ya umarci kawo ƙarshen yajin aikin ASUU, gwamnati na tunanin hana hawa babura

An wallafa

Kamar kowane mako, wannan ma mun duba muhimmai daga abubuwan da suka faru a Najeriya.

Gwamnatin Najeriya na duba yuwuwar hana hawa babur

Babura

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba yuwuwar hana amfani da babura domin dakile ayyukan masu satar mutane da ‘yan ta’adda.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya sanar da haka a karshen taron Majalisar Tsaron ta Ƙasa, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Alhamis a Abuja.

A jawabin nasa ga manema labarai, ministan wanda ke tare da takwaransa na ma’aikatar cikin gida Rauf Aregbesola da kuma na ma’aikatar kula da harkokin ‘yan sanda Alhaji Maigari Dingyadi, ya ce, gwamnati na tunanin hana amfani da baburan da kuma aikin hakar ma’adanai.

Ya ce za ta yi hakan ne domin dakile hanyoyin da ‘yan ta’adda da masu satar mutane ke samun kudade da kuma jigilar kayayyakinsu.

Ministan ya bayyana cewa amfani da baburan na bai wa ‘yan ta’adda damar jigilar kudade da suke samu daga aikin hakar ma’adanai, su sayi makamai.

Sai dai kuma Malamin bai bayyana inda dokar za ta shafa ba, walau kasar baki Daya ko kuma wani bangare na kasar.

Da yake nasa jawabin ministan cikin gida Aregbesola ya ce duk da irin tarin bayanan sirrin da aka yi kafin harin da aka kai kan gidan yari na Kuje ranar 5 ga watan nan na Yuli, ‘yan ta’adda sun samu nasara saboda babu kudurin yakar su, kamar yadda ya ce.

Ya kara da cewana baw a Shugaba Buhari rahoton farko-farko na binciken da aka yi kan harin, tari da alkawarin cewa duk jami’in da aka samu da sakaci a aikinsa za a hukunta shi.

'Yan bindiga sun kashe fasto a Kaduna bayan karɓar kuɗin fansa

Rabaran John Mark Cheitnum

Asalin hoton, Nigerian Catholics

Ƴan bindiga sun kashe ɗaya daga cikin faston cocin katolika a Kaduna da aka sace bayan sun karɓi kuɗin fansarsa.

A wata sanarwa da cocin katolikan ta fitar, ta ce an gano gawar Rabaran John Mark Cheitnum a ranar Talata.

Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Kaduna ya shaida wa BBC cewa masu garkuwa da mutanen sun karɓi kuɗin fansa.

Ya ce bayan da suka karɓi kuɗin fansar sai suka yi musu kwatancen wurin da gawar faston take.

Sai dai ƴan bindigar sun saki ɗayan faston da suka yi garkuwa da shi wato Rabaran Donatus Cleopas.

Babu tabbaci kan dalilin da ya sa aka harbe ɗayan faston. An yi garkuwa da fastocin biyu ne a ƙauyen Yadin Garu a ranar Juma'ar da ta gabata.

Tun daga watan Mayun bana, an yi garkuwa da gwamman malaman Addinin Kirista waɗanda akasarinsu mabiya ɗariƙar katolika ne.

Buhari ya ba da umarnin kawo ƙarshen yajin aikin ASUU

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga ministan ilimi na ƙasar Mallam Adamu Adamu da ya kawo ƙarshen yajin aikin malaman jami'o'in ƙasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Talata inda ya bayar da umarni ga ministan ilimin ƙasar da ya sasanta abubuwan da ake taƙaddama a kai sannan a kai masa rahoto.

Wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar ta ce ministan ilimin ya nemi Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya zare hannunsa daga tattaunawa da ƙungiyar malaman, kuma ya buƙaci abin da bai wuce mako biyu ba don cimma matsaya da su.

Ƙungiyar malam jami'a a Najeriya ta ASUU ta shafe wata kusan biyar tana yajin aikin.

A ranar Talatar Buhari ya tattauna da ma'aikatu da masu ruwa da tsaki waɗanda ke da alaƙa da ɓangaren ilimi a ƙasar da za su iya warware wannan tirka-tirkar.

Shugaban ya kira su ne domin ya samu ƙarin bayani kan dalilin da ya sa wannan yajin aikin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Mutum 30 sun kone a mummunan hatsarin mota a Kaduna

Hatsarin mota a Kaduna

Asalin hoton, Other

Hukumomi a Najeriya sun ce akalla mutum 30 ne suka mutu, wasu gommai kuma suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

Hatsarin ya ritsa da motocin daukar fasinja uku, wadanda suka kama da wuta bayan sun yi taho-mu-gama ranar Alhamis da yamma a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kano.

Babban kwamandan hukumar kiyaye hadura ta kasar reshen jihar Kaduna, Hafiz Muhammad ya shaida wa BBC cewa cikin wadanda lamarin ya ritsa da su har da mata da kananan yara.

Lamarin ya faru ne a daidai wajen da motoci ke aron hannu a inda ake aikin gyaran babbar hanyar.

Jami'ai sun ce rashin hakurin direbobi ne ya haddasa hatsarin.

An tsare tsohon Akanta Janar Ahmed Idris a gidan yarin Kuje

Ahmed Idris

Asalin hoton, Other

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja babban birnin Najeriya ta bayar da umarnin tsare tsohon Babban Akanta na Ƙasa Ahmed Idris a gidan yarin Kuje.

Kotun ta bayar da umarnin kai Mista Idris kurkukun ne bayan hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa, EFCC, ta gurfanar da shi da mutum biyu da kuma wani kamfani a gabanta ranar Juma'a bisa zargin su da sata da kuma zamba-cikin-aminci ta kimanin naira biliyan 109.

Mutanen da aka gurfanar a gaban kotun su ne Ahmed Idris, Godfrey Olusegun Akindele, Mohammed Usman da kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.

A watan Mayun da ya gabata ne EFCC ta kama babban akanta na kasar bayan ya ƙi amsa gayyatar da ta riƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da take yi masa, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Hukumar na zargin Ahmed da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi.

EFCC ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja.

Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya zama na 'yan kasuwa

Buhari da Mele Kyari

Asalin hoton, NNPC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin mai na kasar wanda aka sauya wa fasali, inda a yanzu kamfanin na NNPC ya koma na 'yan kasuwa kuma mai zaman kansa.

An yi kaddamarwar ce a wani kwarya-kwaryar biki a Abuja babban birnin kasar ranar Talata.

Shugaba Buhari ya fara ne da gode wa mahartar taron, wanda ya kira shi da ''mai dimbin tarihi''.

A jawabin da ya gabatar a wurin taron, Shugaba Buhari ya ce an mayar da ikon gudanar da kamfanin ga 'yan kasuwa ne, saboda inganta shi, don samar wa kasar makashin da take bukata.

Ya kuma kara da cewa ''daga yanzu kamfanin NNPC ya koma karkashin gudanarwar 'yan kasuwa, zai kasance kamfani mai zaman kansa ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa a fadin duniya, domin ci gaba da bunkasa hannayen jari sama da miliyan 200 tare da habaka fannin makashi a fadin duniya''.

''A yanzu doka ta dora wa kamfanin alhakin tabbatar da samar wa Najeriya wadataccen makashin da take bukata domin samun habakar tattalin arzikin ta hanyar farfado da wasu fannonin da ke bukatar makashin," in ji Shugaban.