'Yan wasan da Real Madrid ta sayar da tsada a tarihi

Casemiro

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta gabatar da Casemiro a matakin sabon dan kwallon da ta dauka a bana daga Real Madrid.

Dan Brazil, wanda ya yi ban kwana da kungiyar Sifaniya a ranar ta Litinin, ya kalli karawar da United ta doke Liverpool 2-1 a wasan Premier League.

Wasan farko kenan da United ta yi nasara a bana, karkashin sabon koci, Erik ten Hag, bayan da ta sha kashi a hannun Brighton da Brentford.

Dan kwallon tawagar Brazil, mai shekara 30 ya ce ya koma daya daga babbar kungiya a fannin tamaula a duniya, yana da sha'awar daukar Premier League.

United ta sayi dan wasan kan yuro miliyan 70, kan yarjejeniyar kaka hudu, wanda zai zama 'yan gaba-gaba masu karbar albashi a Old Trafford.

Casemiro shi ne na uku da Real Madrid ta sayar mafi tsada a tarihin kungiyar, bayan Cristiano Ronaldo da Angel Di Maria.

Ya koma Sifaniya da taka leda daga Sao Paulo a 2013, Casemiro ya dauki Champions League biyar a Real Madrid da La Liga uku da Cope del Rey daya.

Ya buga Champions League a bara da Real ta doke Liverpool ta lashe kofin Zakarun Turai na 14 jumulla, wanda ya yi mata wasa 336.

Kawo yanzu United ta dauki 'yan kwallo da suka da hada da Tyrell Malacia daga Feyenoord da Christian Eriksen, wanda kwantiraginsa ya kare a Brentford da kuma Lisandro Martinez daga Ajax.

Jerin 'yan wasa 10 da Real Madrid ta sayar da tsada a tarihi

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

1.    Cristiano Ronaldo

Kakar tamula: 18/19        

Kungiyar da ta dauke shi: Juventus

Gasar da ya koma bugawa: Serie A

Kudin da aka sayar da shi: €117.00m

 

2.    Angel Di Maria

Kakar tamaula: 14/15      

Kungiyar da ta dauke shi: Manchester United          

Gasar da ya koma buga wa: England Premier League

Kudin da aka sayar shi: €75.00m

 

3.    Casemiro     

Kakar tamual: 22/23        

Kungiyar da ta dauke shi: Manchester United          

Gasar da ya koma bugawa: England Premier League

Kudin da aka sayar da shi: €70.65m

 

4.    Alvaro Morata        

Kakar tamaula: 17/18      

Kungiyar da ta dauke shi: Chelsea

Gasar da ya koma bugawa: England Premier League

Kudin da aka sayar dda shi: €66.00m

 

5.    Mesut Ozil   

Kakar tamaula: 13/14      

Kungiyar da ta dauke shi: Arsenal

Gasar da ya koma bugawa: England Premier League

Kudin da aka sayar da shi: €47.00m

 

6.    Mateo Kovacic       

Kakar tamaula: 19/20      

Kungiyar da ta dauke shi: Chelsea

Gasar da ya koma bugawa: England Premier League

Kudin da aka sayar da shi: €45.00m

 

7.    Achraf Hakimi        

Kakar tamaula: 20/21      

Kungiyar da ta dauke shi: Inter Milan  

Gasar da ya koma bugawa: Serie A

Kudin da aka sayar shi: €43.00m

 

8.    Robinho       

Kakar tamaula: 08/09      

Kungiyar da ta dauke shi: Manchester City   

Gasar da ya koma buga wa: England Premier League

Kudin da aka sayar da shi: €43.00m

 

9.    Raphael Varane     

Kakar tamaula: 21/22      

Kungiyar da ta dauke shi: Manchester United          

Gasar da ya koma bugawa: England Premier League

Kudin da aka sayar da shi: €40.00m

 

10.Gonzalo Higuain    

 Kakar tamaula: 13/14      

Kungiyar da ta dauke shi:  Napoli

Gasar da ya koma bugawa: Serie A

Kudin da aka sayar da shi: €39.00m