Ana bincike kan yadda duwatsun da ke yawo a samaniya suka kawar da kakannin ƙadangaru daga duniya

Dinosaur

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Masana kimiyya da ke Burtaniya na bincike kan yiwuwar ko ba dutse irin wanda ke yawo a sararin samaniya ɗaya ne kawai ya yi sanadin mutuwar kakannin ƙadangaru ba a lokacin da ya faɗo duniya, wataƙila duwatsu biytu ne suka yi sanadin hakan.

An daɗe da gano cewa wani ƙaton rami da ke binne a ta wajen Mashigin Mexico ya samo asali ne sakamakon faɗuwar da ƙatoton dutsen da ya faɗo daga sararin samaniya da ya yi a wajen shekara miliyan 66 da suka wuce.

Amma masu bincike a Jami'ar Edinburgh Heriot Watt sun ce sun sake gano wani ƙatoton ramin a gefen tekun Atalantika mai irin yawan shekarun.

Sun ce akwai wata alamar cewa dutsen samaniyar ne ya yi sanadin wani ƙaton ramin wanda ke ƙarƙashin teku - a gaɓar tekun Guinea a yammacin Afirka.

Sun ce mai yiwuwa wani ɓangaren dutsen ne ya faɗa sashen Mashigin Tekun Mexico, amma ba za su tabbatar ba har sai sun binciki na tekun Guinea din tukunna.