Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG ta nace wa Nico Williams, Iheanacho zai koma Sevilla
Ɗanwasan tsakiya na Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 28, ya faɗa wa Manchester City cewa yana son raba gari da ita, yayin da Everton da Aston Villa ke buƙatarsa. (Football Insider)
Ɗanwasan gaba na Nigeria Kelechi Iheanacho, mai shekara 27, na dab da kammala yarjejeniya da Sevilla bayan ƙarshen kwantaraginsa da Leicester City. (Sky Germany)
Paris St-Germain na ci gaba da ƙoƙarin yadda za ta karɓo ɗanwasan Athletic Bilbao da Spain Nico Williams, mai shekara 22. (RMC - in French)
Aston Villa na son karɓo ɗanwasan gaba na Barcelona da Brazil Raphinha, mai shekara 27 a wannan bazarar (Football Insider)
Liverpool da Tottenham sun shiga hamayya da Arsenal kan farautar ɗanwasan gaba na Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26 daga Sporting Lisbon. (Football Insider)
Har yanzu ciniki bai faɗa ba tsakanin Aston Villa da Atletico Madrid kan ɗanwasan gaba na Portugal Joao Felix, mai shekara 24. (Fabrizio Romano)
Newcastle sai ta biya fam miliyan 33.73 idan tana son karɓo ɗanwasan baya na Jamus mai shekara 22 Malick Thiaw daga AC Milan. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Arsenal da Chelsea na shirin hamayya da juna domin karɓo ɗanwasan gaba na Manchester City da Argentina Julian Alvarez, mai shekara 24. (TeamTalk)
Leicester City da Southampton na son ɗanwasan Liverpool da Scotland Ben Doak, mai shekara18, idan har ƙungiyar na son bayar da shi aro. (The Athletic - subscription)
Manchester United na ci gaba da tattaunawa da Bayern Munich kan ɗanwasan baya na Netherlands Matthijs de Ligt, mai shekara 24 da kuma ɗanwasan baya na Morocco mai shekara 26 Noussair Mazraoui, waɗanda dukkaninsu ke son zuwa Old Trafford. (Florian Plettenberg - Sky Germany)
Liverpool har yanzu ba ta haƙura ba da ɗanwasan tsakiya na Ingila ba Anthony Gordon, mai shekara 23, duk da Newcastle ba ta son rabuwa da shi a yanzu (Sunday World)
Girona da Tottenham na shirin kammala yarjejeniya kan ɗanwasan gaba na Spain Bryan Gil, mai shekara 23, wanda ke shirin komawa taka leda a La Liga a matsayin ɗanwasan aro. (Fabrizio Romano)