Ƙungiyoyin Saudiyya na neman Salah, Man City ta daidaita da Paqueta

Mohamed Salah

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Kungiyoyin gasar Saudiyya za su kara kwallafa ransu a kan Mohamed Salah a wannan bazara, inda Al-Ittihad za ta taya dan gaban na Liverpool, da Masar mai shekara 31 fam miliyan 70 . (Talksport)

Chelsea na neman yi wa abokan gogayyarta shigar sauri ta saye dan gaban Athletic Bilbao Nico Williams na Sifaniya mai shekara 21tun ma kafin a bude kasuwar 'yanwasa. (Football Insider)

Manchester City ta cimma yarjejeniya da dan wasan tsakiya na West Ham, Lucas Paqueta kafin cinikinsa a lokacin bazara. A bara an yi ta maganar cewa dan wasan na tawagar Brazil mai shekara 26 zai tafi kungiyar. (Foot Mercato)

Liverpool ta bai wa kociyan Sporting Lisbon, Ruben Amorim kwantiragin shekara uku domin maye gurbin Jurgen Klopp a Anfield. (Pedro Sepulveda, ta GiveMeSport)

West Ham ta bi sahun Liverpool, da Tottenham da kuma AC Milan wajen neman dan bayan Fulham Tosin Adarabioyo, wanda zai kasance ba shi da kungiya a bazara. (Guardian)

Tsohon dan wasan Chelsea William Gallas ya ce ya kamata kungiyar ta jarraba neman dan wasan tsakiya na Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 29, da kuma Marcus Rashfor daga Manchester United a wannan bazara. (Mirror)

Chelsea ba ta da ra'ayin sayen mai tsaron ragar Athletico Paranaense, Bento, to amma kuma Inter Milan da ke sonshi za ta fuskanci gogayya daga akan dan wasan na Brazil. (Gazetto dello Sport)

Borussia Dortmund na sha'awar sayen matashin dan wasan gaba na gefe na

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

PSV Eindhoven Johan Bakayoko. Haka kuma rahotanni na cewa Burnley da Brentford ma na son dan tawagar ta Nethrelands. (Voetbal International)

Dan bayan Everton da Ingila Jarrad Branthwaite ya ce yana kokarin hana baza jita-jitar da ake yi a kan makomarsa, kasancewar Manchester United da Real Madrid na sonshi. (90min)

Haka kuma Everton din za ta sa ran samun tayi a kan dan wasanta na tsakiya na Belgium Amadou Onana inda tsohon shugaban Everton Keith Wyness ke cewa kungiyar za ta iya samun wajen fam miliyan 70 a kan dan wasan mai shekara 22, wanda Arsenal, da Newcastle United da kuma West Ham suke so. (Football Insider)

Paris St-Germain ba ta karaya ba kan sayen matashin dan wasan tsakiya na Barcelona da Sifaniya Gavi a bazaran nan, duk da cewa mai shekara 19 yana da sharadin sayar da shi a bazaran nan a kwantiraginsa a kan yuro biliyan daya (L'Equipe )

Tsohon dan wasan tsakiya na West Ham Felipe Anderson na dab da cimma yarjejeniyar tafiya Juventus kyauta. Kwantiragin, dan Brazil din mai shekara 30 zai kare a Lazio a karshen kaka. (Fabrizio Romano)

Kociyan Real Betis Manuel Pellegrini bai gana da jami'an Roma a kan tafiyarsa Stadio Olimpico, inda dan Chilen mai shekara 70 a kwanan an ya ziyarci babban birnin Italiya domin hutun iyalansa