Elliott ya shiga mataki na biyu a shirin sayar da Man United

An wallafa

Kamfanin zuba jari mai suna Elliott Investment Management ya shiga mataki na biyu a shirin sayar da Manchester United.

Wakilan kamfanin Amurka sun kalli wasan da United ta doke Real Betis 4-1 a Old Trafford a gasar Europa League ranar Alhamis.

Shi kamfanin ba yana kokarin sayen United bane, sai dai zai taimakawa masu son sayen kungiyar ko kuma iyalan Glazer idan sun yanke shawarar ci gaba da gudanar da United.

A cikin watan Nuwamba, iyalan Glazer suka ce suna duba hanyar watakila su sayar da Manchester United.

Masu zawarcin sayen United a yanzu haka sun hada da Sir Jim Ratcliffe ta kamfaninsa mai suna Ineos da wani dan kasuwa dan kasar Qatar Sheikh Jassim bin Hamad Al Thani.

Elliott Group ya mallaki AC Milan a baya daga nan ya sayar da kungiyar ga RedBird Capital a Agustan 2022.

United ta lashe Carabao Cup, kofin da ta dauka a karon farko tun bayan 2016/17 karkashin Jose Mourinho da ta dauki League Cup da Europa.

Kungiyar Old Trafford na taka rawar gani a bana karkashin koci, Erik ten Hag da ta dauka kafin fara kakar bana.

United tana ta uku a Premier League a bana, sannan tana quarter finals a FA Cup da za ta buga da Fulam, haka kuma ta doke Real Betis 4-1 a wasan farko zagayen 'yan 16 a Europa League.