Likitoci sun yi wa Neymar tiyata cikin nasara

Neymar

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Wasu kwararrun likitoci a Qatar sun yi wa Neymar tiyata cikin nasara a raunin da yake fama da jinya a kafarsa ta hagu in ji Paris St Germain.

Ana sa ran dan kwallon tawagar Brazil, zai yi jinya zuwa karshen kakar bana, sai a farkon badi kenan zai koma taka leda.

Mai shekara 31 da ke murza leda a PSG, an shiga da shi asibitin Aspetar a Doha yana dingisawa da sanduna ranar Juma'a, inda aka kammala aikin cikin awa daya.

''An yi wa Neymar tiyata cikin nasara da sanyin safiya,'' in ji Paris St germain.

Sai dai PSG ko kuma Aspetar ba wadda ta sanar ko Neymar ya bar asibitin zuwa gida jinya.

An yi aikin ne karkashin wani kwararre dan Birtaniya, James Calder, wanda ya yi wa fitattun 'yan wasan tamaula musamman na turi tiyata a irin raunin da Neymar ya ji.

Neymar zai y jinyar wata hudu ko fiye da haka a raunin da ya fama a wasa da Lille a gasar Ligue 1 a watan jiya.

Yawan raunin da Neymar ke ji shine matsalar da PSG ke fuskanta da dan wasan tun bayan da ta dauko shi daga Barcelona kan $264m a 2017.

Ya buga wa PSG wasanni kaso 49 cikin dari a fafatawar Ligue 1 wato guda 112 daga 228 da ya kamata ya yi tun bayan da ya koma kungiyar da murza leda.

Ko a kakar 2018 likitoci sun yi wa Neymar aiki a dai kafarsa ta hagu da yake yawan fama ta a tamaula.