Ko dai yanzu Man City ta fi karfin Man United ne?

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta yi rashin nasara a gida a hannun Manchester City da ci 3-0 a wasan hamayya a gasar Premier League ranar Lahadi.
Erling Haaland ne ya fara cin kwallo a minti na 26 da fara tamaula, karon farko da City ta samu fenariti a Old Trafford a Premier League a karawa 27.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Haaland ya ƙara na biyu kuma na 20 da ya zura a raga a wasannin waje, shi ne kan gaba a wannan bajintar a fafatawa 13.
Kevin Philips ne mai biye da shi a wannan bajintar, mai kwallo 20 a waje a karawa 28, sai Ian Wright a fafatawa 31 da Diago Costa a gumurzu 33 da kuma Pierre-Emerick Aubameyang shi ma a wasa 33.
Saura minti 10 a tashi daga karawar City ta zura kwallo na uku a raga ta hannun, Phil Foden, hakan ya tabbatar da maki uku ga ƙungiyar Etihad.
Kenan United ta yi rashin nasara biyar daga wasa 10 da fara kakar bana, karon farko da ta yi haka tun bayan 1986/87.
Wasa na 37 kenan da ba a cin Man City da zarar Rodri ya buga mata tamaula, rabon da ta yi rashin nasara a lig tare da ɗan ƙwallon a cikin fili tun Fabrairun 2023 da Tottenham ta yi nasara.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan shi ne karo na bakwai da Guradiola ya ci wasa a Old Trafford ta biyu da ya doke da yawa a karawar waje, bayan Arsenal da ya ci karo takwas a Emirates.
Tun bayan da Guardiola ya karɓi aikin horar da City a 2016 ya hada maki 145 fiye da United, yana da 649 ita kuwa tana da 504.
Haka kuma Guardiola ya ci wasa 60 a Premier League fiye da United, kenan ya ci karawa 205 United ta yi nasara a 145.
Haka kuma kociyan ɗan ƙasar Sifaniya ya ci kwallo 229 fiye da ƙungiyar Old Trafford, kenan ya hada 681 ita kuwa United tana da 452.












