Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An dakatar da 'yan wasan PSG kan rera wakar batanci
An dakatar da 'yan wasan PSG Ousmane Dembele da Randal Kolo Muani da Layvin Kurzawa da kuma Achraf Hakimi wasa daya saboda rera wata wakar batanci.
Kwamitin ladabtarwa na gasar kwalon kafar Faransa (LFP) ya dauki matakin ne bayan an dauki hoton ‘yan wasan suna rera wakar batanci ga magoya bayan Marseille bayan nasarar da PSG ta yi kan abokan karawarsu da ci 4-0 a ranar 24 ga watan Satumba.
A gefe guda kuma, PSG za ta kuma rufe wani gefe na filin wasan Parc des Princes na wasa daya sakamakon yadda magoya bayanta suka yi wa ’yan wasan Marseille wakokin cin zarafi.
'Yan wasan Faransa Dembele, da Muani da Kurzawa, tare da dan wasan baya na Maroko Hakimi, sun nemi afuwar abin da suka aikata ranar Lahadin da ta gabata, suna masu cewa murnar nasarar ce ta dauke masu hankali.
An jinkirta dakatar da 'yan wasan muddin ba su sake aikata wani laifi ba.
Hukuncin rufe gefen filin wasan ya shafi wasanni biyu ne, amma an jinkirta na wasa daya.
PSG ta bayyana hukuncin a matsayin abin da ya wuce gona da iri amma ta ce ba za a daukaka kara ba.