Mbappe da Dembele za su buga wasan PSG da Tolouse

Asalin hoton, Getty Images
Kocin PSG Luis Enriqu ya ce a shirye Kylian Mbappe da Ousmane Dembele suke su fara wasan da ƙungiyar za ta kara da Toulouse ranar Asabar.
Mbappe, mai shekaru 24, ya sake komawa ƙungiyar bayan an ɗauki lokaci ana takun-saka tsakaninsa da Kungiyar sakamakon tabarbarewar mu'amulla kuma yanzu ana tunanin cewa zai iya tsawaita kwantiraginsa.
A farkon makon nan ne Neymar ya bar PSG ya koma kungiyar Al-Hilal ta Saudi Pro League, kwanaki kadan bayan PSG ta sayi Dembele mai shekara 26 daga Barcelona.
An cire Mbappe cikin tawagar a wasan farko da PSG ta buga da Lorient inda aka tashi 0-0 a makon da ya gabata, bayan da bai sami bin kungiyar zuwa atisayen tunkarar kakar wasan bana a yankin Asiya ba.
Dan wasan da ya lashe gasar cin kofin duniya ta 2018 ya kasance abin sha'awa ga Al-Hilal, haka kuma ana alakanta shi da komawa manyan kungiyoyin Turai, har sai da aka samu sauyin yanayi aka sami sasantawa tsakanin dan wasa da ƙungiyar.
Al-Hilal ta sayi Neymar mai shekaru 31, kan kudi Yuro miliyan 90, kuma tsohon dan wasan Santos da Barcelona za a biya shi Yuro miliyan 150 kowane shekara a Saudiyya.
Enrique ya ce tafiyar Neymar abu ne mai kyau ga duk wanda abin ya shafa.







