Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Guardiola na shirin tsawaita zamansa a City, Barca ta yi watsi da tayin PSG kan Lamine Yamal
Pep Guardiola na shirin tsawaita zamansa a Manchester City, Barcelona ta yi watsi da babban tayin Lamine Yamal a bazara, Manchester United na zawarcin Frenkie de Jong.
Kocin Manchester City Pep Guardiola na iya rattaba hannu kan tsawaita kwantiraginsa ko da kulob din ya yi rashin nasara a shari'ar da yake yi kan zargin keta dokokin kudi har guda 115. (Athletic)
Kocin nan dan kasar Portugal Ruben Amorim mai shekara 39, da kocin Bayer Leverkusen dan kasar Sipaniya, Xabi Alonso, mai shekara 42, su ne kan gaba a jerin sunayen da Manchester City ke nazari a kansu don maye gurbin Guardiola idan ya yanke shawarar barin kungiyar. (Mail)
Barcelona ta yi watsi da tayin Yuro miliyan 250 daga Paris St-Germain a bazara kan dan wasan gefe na Spain Lamine Yamal mai shekaru 17. (Goal)
Arsenal da Manchester City na cikin masu sha'awar dan wasan Atalanta mai shekara 23 dan kasar Belgium Charles de Ketelaere. (Caught Offside)
Kocin Manchester United Erik ten Hag na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 27, a watan Janairu yayin da yake kokarin sake gina tsakiyarsa. (Sport Spanish)
Manchester United na zawarcin dan wasan gaban RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 21, wanda ake sa ran zai bar kungiyar ta Bundesliga a bazara mai zuwa. (Mail)
Barcelona na zawarcin dan wasan Bayer Leverkusen kuma dan bayan Jamus Jonathan Tah, mai shekara 28, dan kasar Canada da Bayern Munich Alphonso Davies, mai shekara 23, da dan wasan gaban Lille da Canada Jonathan David, mai shekara 24. (Mundo Deportivo)
Kociyan Italiya Carmine Nunziata ya shawarci dan wasan tsakiya na Chelsea Cesare Casadei, mai shekara 21, da ya yi la'akari da makomarsa a Blues a watan Janairu idan ba zai rika samun lokacin wasa ba. (Rai Radio 1 via Metro)