Man Utd na son Martinez, Diaz na son barin Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na nazarin ɗauko golan Aston Villa Emi Martinez amma sai ta biya farashin golan na Argentina mai shekara 32 fam miliyan 40. (Mail)
Ɗanwasan gaba na Colombia Luis Diaz, mai shekara 28, ya nace cewa yana son barin Liverpool inda yake fatan Bayern Munich za ta sake shigar da sabon tayinsa. (ESPN)
Manchester City na shirin shan gaban Newcastle kan golan Burnley da England James Trafford. (Telegraph - subscription required)
Trafford ya fi son ya dawo City a wannan bazara idan ta sha gaban Newcastle. (Football Insider)
Newcastle za ta sabunta kwangilar Tino Livramento don hana shi zuwa Manchester City, da ke shirin lale fam miliyan 65 domin karɓo ɗanwasan na Ingila. (Times - subscription required)
Tottenham za ta shiga hamayya da Liverpool kan ɗanwasan Crystal Palace da Ingila mai shekara 25 Marc Guehi. (Telegraph - subscription required)
Fatan Manchester United kan Nicolas Jackson ya ƙaru bayan ɗanwasan na Chelsea da Senegal mai shekara 24, ya yi watsi da tayin AC Milan da Napoli saboda yana son ci gaba da taka leda a Premier League. (Sun)
Juventus za ta ƙara matsin lamba kan karɓo ɗanwasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25, daga Manchester United idan ɗanwasan Belgium Samuel Mbangula, mai shekara 21, da ɗanwasan Amurka Timothy Weah sun tafi. (Tuttosport - in Italian)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Manchester United na shirin shiga hamayya da Manchester City kan ɗanwasan tsakiya na Sporting da Denmark Morten Hjulmand mai shekaraq 26. (A Bola - in Portuguese),
Chelsea na son ɗanwasan tsakiya na RB Leipzig Xavi Simons, mai shekara 22, amma sai ta sayar da wasu ƴanwasanta kafin buɗe wa ɗanwasan na Netherlands ƙofa. (Telegraph - subscription required)
West Ham na son golan Leicester City Mads Hermansen, kuma tana shirin gabatar da buƙatarta kan golan mai shekara 25. (Sky Sports)
Matashin ɗanwasan tsakiya na Liverpool da Ingila James McConnell, mai shekara 20, na dab da sa hannu kan doguwar yarjejeniya. (Mail)
Sunderland da Fenerbahce na ci gaba da farautar Granit Xhaka duk da Bayer Leverkusen ta yi watsi da buƙatarsu kan ɗanwasan tsakiyar na Switzerland. (Florian Plettenberg)
Napoli da AC Milan da Roma da Juventus da Inter Milan na hamayya kan ɗanwasan Liverpool mai shekara 27 Federico Chiesa. (Calciomercato - in Italian)
Everton ta tattaunawa Real Sociedad kan ɗanwasan Japan Takefusa Kubo. (Teamtalk)












