Real ta rage tazarar maki tsakaninta da Barca ya koma huɗu

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid ta je ta doke Deportivo Alaves 1-0 a wasan mako na 31 a La Liga da suka kara ranar Lahadi a filin Mendizorroza.

Ƙungiyar Santiago Bernabeu ta ci ƙwallon ta hannun Eduardo Camavinga tun kan hutu, haka suka tashi Alaves ta kasa farkewa.

Sai dai Real ta kasara karawar da yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Kylian Mbappe jan kati.

Karo na biyu a jere da aka bai wa ɗan wasan Real jan kati, bayan Camavinga a wasa da Arsenal a Champions League ranar Talata a Emirtaes.

Itama Alaves ta kammala karawa da mutum 10 a fili, sakamakon da aka korar mata, Manu Sánchez, saura minti 20 a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Real mai rike da kofin bara tana mataki na biyu a La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona mai jan ragama mai maki 70.

Ranar Laraba Real Madrid za ta kara da Arsenal a wasa na biyu a Champions League zagayen kwata fainal a Santiago Bernabeu.

A makon jiya Arsenal ta doke Real Madrid 3-0 a Emirates a gasar ta zakarun Turai ta kakar nan.

Ƴan Real Madrid 11 da suka fuskanci Alaves:

1. Courtois

17. Lucas V.

35. Asencio

22. Rüdiger

20. Fran García

8. Valverde

14. Tchouameni

6. Camavinga

15. Arda Güler

9. Mbappé

11. Rodrygo.

Masu jiran ko-ta-kwana:

26. Fran

34. Sergio Mestre

4. Alaba

5. Bellingham

7. Vini Jr.

10. Modrić

16. Endrick

18. Vallejo

19. Ceballos

21. Brahim.

Ɓ ɓ

Ɗ ɗ

Ƙ ƙ

Ƴ ƴ