Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Leicester City da Tottenham sun raba maki a Premier League
Leicester City da Tottenham sun tashi 1-1 a wasan makon farko a Premier League ranar Litinin a King Power.
Pedro Porro ne ya fara ci wa Tottenham ƙwallo a minti na 31 a karawar ta hamayya, kuma haka suka je hutu ana cin Leicester City 1-0.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Jamie Vardy ya kara na biyu, kuma na 17 a Premier League da ya ci Tottenham.
Rabon da su fuskanci juna tun 2022/23, inda Tottenham ta ci 6-2, ita kuma Leicester ta yi nasara 4-1 a King Power.
Kafin wasan nan an ci ƙwallo 128 a karawa 34 a Premier League tsakaninsu. Shi ne wasan da aka fi zazzaga ƙwallaye a raga a haɗuwa sama da 20 a gasar.
Wasa ɗaya ne Tottenham ta yi rashin nasara daga tara kenan a ranar buɗe labulen Premier League, shi ne wanda Everton ta ci 1-0, Tottenham ta ci biyar da canjaras biyu daga ciki.
Kyaftin ɗin Tottenham, Son Heung-min bai ci ƙwallo ba ranar Litinin, wanda ya zura tara a ragar Leicester City da bayar da huɗu aka ci a wasa 15 da ya fuskanci ƙungiyar.
Ƴan wasan da suka buga karawar
An yi mamaki da Leicester City ta fara wasa da Jamie Vardy, wanda kwana ɗaya tsakani koci, Steve Cooper ya ce ɗan ƙwallon na jinya.
Leicester ta fara amfani da Bobby Decordova-Reid, wanda ta ɗauka a bana da wanda ta ɗauka aro daga Brighton, Facundo Buonanotte
Ƴan wasan Leicester City 11: Hermansen, Kristiansen, Faes Vestergaard, Justin, Winks, Ndidi; Buonanotte, Decordova-Reid, Fatawu, Vardy.
Masu jiran ko-ta-kwana: Ward, Ricardo, Nelson, Choudhury, Soumare, McAteer, Mavididi, Cannon, Okoli.
Dominic Solanke ya fara yi wa Tottenham tamaula, wanda ta ɗauka a watan nan kan £65m daga Bournemouth.
James Maddison ya je filin King Power Stadium a karon farko tun bayan da ya bar ƙungiyar zuwa Tottenham, bayan da ta faɗi daga Premier League a 2023.
Archie Gray ya fara da zaman benci, wanda ya koma Tottenham daga Leeds United a bana.
Ƴan wasan Tottenham 11: Vicario; Porro, Romero, Van de Ven, Udogie, Bentancur, Maddison, Sarr, Johnson, Solanke, Son.
Masu jiran ko-ta-kwana: Dragusin; Richarlison, Gray, Bergvall, Werner, Spence, Kulusevski, Davies, Austin