Sarewa da hawaye cikin hotunan Afirka na mako

An wallafa

Ga wasu kayatattun hotunan Afirka na mako.

Models prepare backstage for a fashion show at the Durban July horse races in South Africa on Saturday.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Nan masu kwalliya ne ke shirin nuna adonsu a gasar tseren dokuna ta watan Yuli a birnin Durban na Afirka ta Kudu a ranar Asabar.
Israel Adesanya of Nigeria channels US wrestling legend The Undertaker with his trademark hat, ahead of a UFC middleweight bout in Las Vegas on Saturday.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan dan Najeriya, Israel Adesanya, tare da zakakurin dan wasan damben Amurka, Undertaker sanye da hular da aka fi saninsa da ita, gabanin wasan damben ajin masu matsakaicin karfi a birnin Las Vegas, a ranar Lahadi.
Malian music and screen star Fatoumata Diawara performs at a festival in Denmark on Friday.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Nan kuma a ranar Juma'a, mawakiyar kasar Mali, Fatoumata Diawara ke gudanar da wasa a wani biki a Denmark.
Thingo Khumalo, whose mother stars in reality show Life with Kelly Khumalo, poses at the series three launch in South Africa on Saturday.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan, diya ce ga shahararriyar mai fitowa a wani shirin talabijin mai suna 'Reality Show Life' ke daukar hoto yayin kaddamar da shirin karo na uku a Afirka ta Kudu ranar Asabar.
On the same day, well-known street food cook Habib el-Bey gets to work in his van on Habib Bourguiba Avenue, in Tunisia's capital city.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Duk dai a ranar, wani shahararren mai dafa abinci a bakin titi, Habib el-Bey a wajen aiki da ke layin Habib Bourguiba Avenue, a babban birni Tunisia.
On Monday as Eid al-Adha celebrations near, a vendor shows off his healthy livestock at a market in Khartoum, Sudan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Litinin kuwa, yayin da shirye-shiryen bikin Sallah ke karatowa, wani mai sayar da dabbobi ke nuna lafiyar dabbobinsa ga masu saye a wata kasuwa a Khartoum, babban birnin Sudan.
The day before in Cairo, Egypt, blades are lined up at a sharpening shop.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kwana guda kafin nan, a Cairo, babban birnin kasar Masar, an jera wukake a wani shago da ake wasa su domin kara kaifin su.
On Friday these fishermen on South Africa's eastern coast pull their nets in during the annual sardine run.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Juma'a, wadannan masu kamun kifi a wani teku da ke gabashin Afirka ta Kudu na jan ragoginsu yayin wani bikin masu 'Su' da aka saba yi duk shekara.
On Sunday a visitor takes in one of the pieces at Libya's Tra Tani exhibition, described as a puzzle game consisting of artworks by local artist

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan a ranar Lahadi, wani mai ziyara ke kallon hoton wani mai rike da garaya a wani bikin masu zane-zane a kasar Libya.
On Wednesday, Ayanbinrin Aduke drums during the 80th birthday party for Jimi Solanke - a multi-talented dramatist and storyteller - in Lagos, Nigeria.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Laraba kuwa, Ayanbinrin Aduke, ke buga ganga yayin bikin zagayowar ranar haihuwar Jimi Solanke - wata shahararriyar mai wasan dabe da kuma ke yin tatsuniyoyi - a birni Lagos, da ke Najeriya.
On Friday a group of Nigerian musicians performs at a ceremony in Germany for the handover process of stolen colonial-era treasures - known as the Benin Bronzes.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Juma'a, kungiyar wasu mawakan Najeriya ke wasa a wani bikin sake dawowa da Najeriya kayan tarihi da aka sace zamanin mulkin mallaka a kasar Jamus.
Staff tend to Friendship Park in Ethiopia's capital Addis Ababa on Tuesday, ahead of its opening.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan, ma'aikata ne ke aikin tsaftace wani wajen shakatawa a Addis Ababa, babban birnin Habasha a ranar Talata, gabanin bude shi.
On the same in the South African city of East London, mourners pay their respects at a mass memorial service to 21 teenagers who died in a tavern last month.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Duk dai a ranar, a birnin East London na Afirka ta Kudu, masu zaman makoki a wani bikin bankwana ga matasa 21 da suka mutu yayin biki a wani gidan rawa da daddare a wata daya gabata.
On Friday, protesters in Khartoum mark the third anniversary of anti-government demonstrations in Sudan.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Juma'a, masu zanga-zanga a Khartoum ke bikin cika shekara uku da gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a Sudan.
"Black lives matter" and "No human being is illegal" read some of the banners waved by demonstrators in the Spanish enclave of Melilla on Friday, where 23 migrants were killed close to the Morocco border one week ago.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan, masu zanga-zanga ne ke rike da alluna da ke dauke da rubuce-rubucen ''Rayuwar bakaken fata na da muhimmani da ''bai kamata a musgunawa bil-adama ba' yayin wata zanga-zanga ranar Juma'a a yankin Melilla da Sifaniya ke iko da shi, inda aka kashe 'yan cirani 23 a wani wuri kusa da iyaka da Morocco a mako daya gabata.
On the same day, Cameroonian national Agol Tchabda, who gave birth to her baby on a migrant boat in the Mediterranean, is cared for in hospital in Turkey's Aydin province

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duka dai a ranar, a nan, a wani asibiti da ke lardin Aydin na Turkiyya, ana kula da wata 'yar cirani 'yar asalin Kamaru, Angol Tchabda da ta haifu a cikin jirgin ruwa dauke da 'yan cirani a tekun Mediterranean.
And on Tuesday, a man walks up a hill in the Casbah of Algiers, in Algeria.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Talata kuwa, wani mutumi ne ke kokarin hawa wani tsauni a garin Casbah da ke Algiers, babban birnin Algeria.