Arsenal ta ci Everton karo na 100 ta bayar da tazarar maki biyar

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta ci Everton 4-0 a kwantan wasan Premier League da suka kara ranar Laraba a Emirates.

Wasa ne da ya kamata su fafata tun ranar 11 ga watan Satumbar 2022.

Arsenal ta ci kwallo ta hannun Bukayo Saka saura minti biyar su yi hutu, sannan Gabriel Martinelli ya kara na biyu daf da cikar minti na 45.

Kyaftin din Arsenal, Martin Odegaard shine ya kara na biyu, saura minti 19 a tashi daga karawar daga baya Martinelli ya kara na biyu na hudu a wasan.

Wannan shine karo na 100 da Arsenal ta ci Everton a babbar gasar tamaula ta Ingila a wasa 204 da canjars 43, Everton ta yi nasara a 61.

Sun kara ranar 4 ga watan Fabrairu a Goodison Park, inda Everton ta ci 1-0 ta hannun James Tarkowski a minti na 60 a gasar ta Premier.

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama a matakin farko a kan teburin Premier da maki 60, bayan karawa 25 a Premier ta bana.

Karon farko da Gunners ta hada maki 60, bayan wasa 25 a Premier, wadda ta taba yin wannan kwazon a kakar 2003-04 da kuma a 2007-08.

Ta kuma bai wa Manchester City tazarar maki biyar, wadda take ta biyu mai rike da kofin bara.

Everton ta ci gaba da zama a mataki na 18 cikin 'yan ukun karshe a teburin bana da maki 21.