Dokokin da INEC ta fitar game da yin kamfe da na kashe kuɗin jam'iyyu

An wallafa

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta fitar da ƙa'idojin yaƙin neman zaɓe da kuma kuɗin da jam'iyyu da 'yan takararsu za su kashe yayin da ake tunkarar babban zaɓe na 2023.

Shugaban Sashen Wayar da Kan Masu Zaɓe na Independent National Electoral Commission (INEC) Festus Okoye ya ce hukumar ta fitar da ƙa'idojin ne a ranar Alhamis bayan wani taro da masu ruwa da tsaki suka gudanar.

Cikin ƙa'idojin har da adadin kuɗi na gudunmawar da 'yan takara ko jam'iyyunsu za su karɓa daga hannun magoya bayansu.

Kazalika hukumar zaben ta tanadi waɗansu takardu da za ta yi amfani da su wajen bin diddigin hidimar da jam`iyyun siyasar suke yi da kudi.

A watan Fabarairun 2023 INEC za ta gudanar da babban zaɓen, inda 'yan Najeriya za su zaɓi shugaban ƙasa da gwamnoni da 'yan majalisar tarayya da na jiha a mafi yawan jihohin ƙasar.

A wannan shekara ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya saka wa sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022 hannu, bayan an yi wa ta 2010 kwaskwarima.

Jam'iyyar APC mai mulki na fatan sake lashe zaɓen a karo na uku bayan Buhari ya yi wa'adin shekara huɗu sau biyu, yayin da babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke neman sake hawa mulkin bayan ta shafe shekara 16 tana jan ragamar ƙasar.

Ga dokokin da INEC ta gindaya:

Adadin kuɗin gudummuwa

INEC ta fitar da kundin sabbin ƙa'idojin ne ƙari a kan tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2022. Kundin ya ce:

(1) Mafi yawan adadin kuɗi ko na kadara da wani mutum, ko wani rukunin mutane, ko wata ƙungiya, zai bayar a matsayin gudunmawa ga jam'iyyar siyasa ko mai neman takara ba zai wuce naira miliyan 50 ba (N50,000,000).

(2) Kar jam'iyya ta karɓi adadin kuɗin da ya zarta naira miliyan 50 sai dai fa idan za ta faɗa wa INEC inda ta samu kuɗin.

(3) Dole ne gudunmawar da wani ko wata ƙungiya za ta bai wa ɗan takara ta zama daga kwana 150 da aka ware don yin yaƙin neman zaɓe zuwa kafin ranar kaɗa ƙuri'a.

(4) Gudunmawar da wani ko wata ƙungiya za ta bai wa mai neman takara, ta kasance daga ranar da aka kafe sanarwar ranar zaɓe zuwa lokacin kammala zaɓukan fitar da gwani.

Kuɗin da 'yan takara ya kamata su kashe a zaɓe

Haka nan, INEC ta ce bai dace 'yan takara su kashe kuɗin da ya zarta adadin da Dokar Zaɓe ta 2022 ta sharɗanta ba. Sashe na 88 na dokar ya ce:

"(1) Mafi yawan adadin abin da ɗan takarar shugaban ƙasa zai kashe a lokacin zaɓe shi ne naira biliyan biyar (N5,000,000,000).

"(2) Mafi yawan adadin abin da ɗan takarar gwamna zai kashe a lokacin zaɓe shi ne naira biliyan ɗaya (N1,000,000,000).

"(3) Mafi yawan adadin abin da ɗan takarar sanata zai kashe a lokacin zaɓe shi ne naira miliyan 100 (N100,000,000), da kuma naira miliyan 70 (N70,000,000) ga ɗan takarar majalisar wakilai.

"(5) A zaɓen majalisar dokokin jiha kuma, mafi yawan adadin kuɗin da za a kashe shi ne miliyan 30 (N30,000,000).

"(6) A ɓangaren zaɓen shugaban ƙaramar hukuma, mafi yawan adadin kuɗin da za a kashe shi ne naira miliyan 30 (N30,000,000).

"Dangane da zaɓen kansila, mafi yawan adadin kuɗin da ɗan takara zai kashe shi ne miliyan biyar (N5,000,000).

Ba da rahoton kuɗi da kadarori na shekara-shekara na jam'iyyu

Kundin INEC ya kuma umarci dukkan jam'iyyun siyasa a Najeriya da bayyana dukkan samunsu da kuma inda suka samu kuɗin.

Ya ce: "Dole ne kowace jam'iyya ta miƙa wa INEC cikakken rahoto na shekara game da kadarorinta da basukan da ake bin ta, da bayanin inda ta samu kuɗinta da sauran kadarori, haɗi da bayanin yadda ta kashe kuɗin daga 1 ga watan Fabarairu zuwa 30 ga Maris na shekara ta gaba cikin kwafin takarda da na latironi."

Bayyanawa da kuma ƙwace gudunmawar da aka samu daga ƙasar waje

Hukumar zaɓe a Najeriya ta haramta wa jam'iyyu karɓar gudunmawar kuɗi daga ƙasashen waje.

"Dole ne kowace jam'iyya ta sanar tare da aika wa INEC duk wasu kuɗi ko kadara da aka aike mata daga wajen Najeriya cikin kwana 21 da faruwar hakan.

"Idan akwai buƙata, za a nemi jam'iyyar ta gabatar da waɗannan bayanan kamar yadda INEC za ta buƙata."

Rahoton kuɗin da jam'iyya ta kashe a lokacin zaɓe

Bugu da ƙari, kundin ƙa'idojin ya umarci jam'iyyu su gabatar mata da rahoton abin da suka yi da kuɗi matuƙar sun shiga zaɓen da aka kammala.

"Duk jam'iyyar da ta shiga wani zaɓe, wajibi ne ta aika wa shafin da aka tanada na musamman da bayanan abin da ta kashe a lokacin zaɓen cikin wata shida da kammala shi.

"Wajibi ne a fara haɗa rahoton daga kwana 360 zuwa ranar ranar zaɓe."

Bayyana gudunmawar da jam'iyya ta samu don ɗaukar nauyin ɗan takara

"Duk jam'iyyar da ta ɗauki nauyin wani ɗan takara, dole ne ta miƙa wa shafin da aka tanada rahoton gudunmawar da ta samu daga wasu mutane da ƙungiyoyi cikin wata uku da bayyana sakamakon zaɓen.

"Rahoton sai ya ƙunshi sunaye da adireshi da sana'a ta mutanen da suka bayar da gudunmawar da kuma adadin kuɗin."

'Yan takara su adana bayanan gudunmawarsu

"Wajibi ne dukkan jam'iyyu su tabbatar cewa 'yan takararsu sun mallaki cikakken bayani kowace gudunmawa da kuma sauran hanyar samun kuɗi, kuma bayanan su ƙunshi suna da adireshi da sana'ar mutanen da adadin kuɗin.