Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Liverpool ke cin karo da koma baya a Premier a bana?
Liverpool tana mataki na tara a teburin Premier League da maki 16, bayan buga wasa 12 a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.
Kawo yanzu Liverpool ta ci wasa hudu da canjaras hudu aka doke ta karawa hudu, bayan da wasa biyu ta yi rashin nasara a bara da ta yi ta biyu a gasar.
Ranar Asabar Leeds United ta doke Liverpool 2-1 a Anfield a wasan mako na 14 a Premier League.
Karon farko da aka ci kungiyar a filin Anfield tun bayan wasa 29 a jere ba a doke ta ba, rabon da ta yi rashin nasara tun 1-0 da Fulham ta yi a Maris din 2021.
Cikin wasa 29 da ta buga a Anfield ba tare da rashin nasara ba a jere ta ci 22 da yin canjaras bakwai.
Liverpool ta yi rashin nasara a wasa biyu a jere kenan, bayan da tun farko Nottingham Forest ta yi nasara da ci 1-0.
Rashin nasara da Liverpool ta yi a Anfield shi ne karon farko tare da mai tsaron baya Virgil van Dijk a cikin fili, wanda ya yi karawa 70 a gida ba a doke kungiyar ba a gida.
Liverpool za ta buga wasa daya a Premier League, sannan a je gasar kofin duniya, shi ne wanda za ta karbi bakuncin Southampton ranar 12 ga watan Nuwamba.
Daga lokacin Liverpool za ta dan sarara har sai bayan gasar kofin duniya, watakila ta kamo bakin zaren.
To sai dai me ya sa Liverpool ba ta kokari a bana duk da cefanen da ta yi, bayan da ta kare a mataki na biyu a bara da Manchester City ta lashe kofin?
Tun farko wasu na cewar duk inda Jurgen Kloop ya yi shekara bakwai a kungiya ya kan ci karo da kalubale a shekara ta takwas.
Wasu na cewar salon tamaula iri daya yake yi shi ya sa idan ya yi shekara bakwai kowa ke gane dabararsa a fagen horar da tamaula.
Haka ya faru a Mainz da Borussia Dortmund da ya yi kaka bakwai a kowacce kungiyar, amma ya kasa kai bantensa a shekara ta takwas.
Ana ganin cewar yawan rauni da 'yan wasan Liverpool ke yi na daya daga koma baya da kungiyar ke fuskanta.
Wadanda ke jiya kawo yanzu sun hada da Thiago Alcantara da Luis Diaz da Diogo Jota da Ibrahima Konate da Joel Matip da kuma Arthur Melo.
Mohamed Salah baya cin kwallo kamar yadda ya kamata, domin kafin wasa da Leeds uku ya zura a raga mafi karanci, wanda a Oktoban ya kan ci biyar.
Haka kuma ana hasashen cewar wasu 'yan kwallon Liverpool shekara sun ja ya kamata ta kara daukar wasu masu jini a jika ta kara sirkawa.
Ba shakka tafiyar Sadio Mane zuwa Bayern Munich a bana ya taba Liverpool, wadda ta dauko Darwin Nunez, wanda ya maye gurbin dan kwallon tawagar Senegal.
Nunez ya ci kwallo hudu a Premier League ta bana an kuma yi masa jan kati a kakar nan.
To sai dai kuma Liverpool na kokari a Champions League, bayan da ta samu gurbin shiga wasannin gaba na kungiyoyi 16.
Ranar Talata 1 ga watan Nuwamba, Liverpool za ta kara da Napoli a wasan karshe a rukunin farko a gasar zakarun Turai.
A haduwar farko ta cikin rukuni da suka yi a ranar 7 ga watan Satumba Napoli ce ta doke Liverpool da ci 4-1 a Italiya.