Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Benzema ya yi kan-kan-kan da Raul a ci wa Real kwallaye a La Liga
Ranar Lahadi Real Madrid ta je ta ci Athletic Bilbao 2-0 a wasan mako na 18 a gasar La Liga.
Karim Benzema ne ya fara cin kwallo a minti na 24 da fara tamaula, sannan Toni Kroos ya kara na biyu daf da za a tashi daga fafatawar.
Kwallon da Benzema ya ci a filin San Mames ya sa ya yi kan-kan-kan da Raul a tarihin yawan ci wa Real Madrid kwallaye a raga a La Liga.
Dan kasar Faransa ya ci kwallon da yanzu yana da iri daya da ta Raul mai 228, wanda ya yi kwazon nan tsakanin 1994 zuwa 2010, shi ne na biyu a kungiyar.
Wanda yake na daya a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a La Liga shi ne Cristiano Ronaldo mai 312 a raga.
Benzema, wanda keda kwallo tara a babbar gasar tamaula ta Sifaniya a bana, ya fara ci wa Real kwallo a tariihi a karawar mako na uku a kakar 2009/10 a fafatawa da against Xerez.
Kungiyar da Benzema ya ci kwallaye da yawa a La Liga ita ce Getafe da ya zura mata 17, sai Granada da ya ci 14.
Kyaftin din Real Madrid, shi ne kan gaba a zura kwallaye a La Liga a bara da 27, inda kungiyar ta lashe La Liga na 35 jumulla.
Mai rike da Ballon d'Or shi ne na biyu a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a tarihi, mai 335 kawo yanzu a dukkan fafatawa.
Cikin kofuna 23 da ya dauka a Real Madrid sun hada da Champions League biyar da Club World Cup hudu da Uefa Super Cup hudu da La Liga hudu da Copa del Rey biyu da Spanish Super Cup hudu.