Yadda soyayya ke gajiyar da masu yin ta a intanet

An wallafa

Duddubawa, da hirarraki, da haɗuwa da mutane, da basarwa: soyayya ta intanet na gajiyar da samari da 'yan mata.

Andy Hong ji yake kamar mace ɗaya yake ta haɗuwa da ita a intanet kodayaushe.

Ɗan shekara 28 ɗin da ya kammala makaranta a New England kuma masoyin ƙwallon ƙafa, ya ce ba shi da matsala da wajen haɗuwa da matar amma fa hakan ba ya nufin son ta yake yi, kuma ya yi imanin akwai wasu matan da zai iya yin soyayya mai daɗi da su fiye da ita.

Ya gaji da irin wannan soyayya, amma har yanzu manhajar soyayyar intanet mai suna Hinge na ci gaba da nuno masa 'yan mata masu siffa iri ɗaya.

"Za su nuna maka wasu iri kuma su turo maka wasu daban," a cewar Hong mazaunin Boston na Amurka game da manhajar ta Hinge.

Hong ya bayyana irin wannan yanayi da "tataɓurzar yanke hukunci" - wasu kuma na kiran sa "gajiyarwar soyayyar intanet".

Abu ne da masu soyayya a intanet da ke amfani da manhjojin da ake kira dating app a turancin Ingilishi ke fuskanta a rayuwarsu, wani zubin ma har su gaji da duddubawa don neman saurayi ko budurwa.

"Idan ana maganar adadin mutane, idan aka haɗa ka da mutum kamar 10, akwai yiwuwar ka yi magana da bakwai ko takwas daga cikinsu," a cewar Hong.

"Daga cikin waɗannan adadin, za ka iya haɗuwa da ɗaya ko biyu."

A 'yan kwanakin nan ana yayin amfani da manhajojin soyayya, inda wani bincike da aka yi a 2019 ya gano cewa akwai yiwuwar masoya su haɗu ta nan fiye da sauran hanyoyi.

Sai dai kuma ba abu ne mai sauƙi ba: wani bincike da manhajar Badoo ta gudanar a Birtaniya ya ce fiye da kashi uku cikin huɗu na samari da 'yan mata na fuskantar gajiya sakamakon yawan haɗuwa da masoyan da ba sa ba su dace da su ba da kuma yadda manhajojin ke yawan yi musu tallan mutane.

Ita ma manhajar Hinge ta gano cewa kashi 61 na masu amfani da ita na shan fama da yadda manhajojin ke aiki.

Yayin da wani binciken a watan Afrilun 2022 daga Amurka ya bayyana cewa "masu amfani da manhajojin kan haɗu da gajiyar ƙwaƙwalwa saboda amfani da su".

Sai dai duk da haka mutane na ci gaba da amfani da manhajojin don neman masoya, kuma da alama duk irin yadda suke da wahala mutane sun fi samun abin da suke so cikin sauƙi ta nan ɗin.

‘Akwai yawan duddubawa’ 

A taƙaice, gajiyar soyayyar intanet na nufin gajiyar da mutane ke fama da ita saboda yawan dudduba abubuwa a manhajar soyayya ta intanet, a cewar Nora Padison, wata ƙwararriyar mai ba da shawara a kamfanin Space Between Counseling Services da ke Amurka.

Padison ta ce ana iya fahintar wannan gajiya lokacin da mutum ya fara munana zato kan manhajojin soyayyar; da lokacin da ya fara jin abin ya zamar masa wani aikin yi, in ji Padison.

A cewar wani bincike na Leah LeFebvre, farfesa a fannin sadarwa na Jami'ar Alabama, fiye da rabin mutum 395 da ke amfani da manhajar Tinder da ta yi bincike a kan su a 2017 sun sha goge manhajar daga wayarsu a lokuta da dama.

Kashi 35 na mutanen sun ce sun goge manhajar ce saboda ba su samu abin da suke so ba.

Hakan na nufin ko dai ba su samu amsa ba, ko ba su samu wanda ya dace da su ba, ko kuma ba su samu amsar da suke so ba," in ji Padikson.

Guiser ta fara amfani da manhajar Bubmble da Hinge lokacin da ta katse soyayyar da take yi a watan Janairu, duk da cewa tun a 2013 ta fara amfani da manhajojin.

Tsarin manhajojin soyayya ka iya haifar da ƙunci ga masu amfani da su waɗanda da ma suke a gajiye.

Guiser ta gaji da wasu tsarukan manhajar da ka iya kyautata amfani da ita. Misali, takan kalli aƙidar siyasa ta mutumin da aka haɗa ta da shi kafin komai.

Sai dai ta ce a manhajar Bumble, dole sai mutum ya biya sannan zai iya zaɓar mutane bisa tsarin da ya fi so.

Amma tun da ita ba kuɗi take biya ba, "an tilasta mata dudduba ɗaruruwan mutanen da take son haɗuwa da su".

Abu ne kuma mai rikitarwa idan mutum yana duba manhajojin soyayya da yawa a lokaci guda, amma mutane da yawa kan haɗa fiye da ɗaya saboda suna tsammanin za su fi saurin samun masoyi.

"Sai bayan na saba da wata manhajar sai kuma na buɗe wata, sai in ji irin 'ah na wuce wani da ya kamata na so shi, ko kuma 'yanzu na wuce wani da nake so wanda hotonsa kawai na zo gani'," a cewar Guiser.

Akwai kuma ƙalubalen hira da mutumin da taku ta zo ɗaya.

Wannan matakin na ƙunshe da wasu sabbin wahalhalu, saboda wasu kan nuna halayen rashin kyautawa a kan manhajar.

Ci gaba ko kuma ɗaukar hutu

Duk da balahirar da suke fuskanta, akasarin masu amfani da manhajar, kamar Hong, sun ci gaba da amfani da shi.

"Za ku iya kwatanta su [manhajojin soyayya] da shafin Amazon," a cewar Padison, "ta yadda mutane sun fi son su yi amfani da manhajojin soyayya sama da su haɗu da mutane a zahiri ko da kuwa mutane ba sa ƙaunar manhajar sosai."

Annobar korona ta ƙara saka mutane shiga yin hirarraki ta intanet kuma suke jin gara su tantance mutanen da suke so tun kafin su haɗu da su.

Haka nan kuma, ba abu ne mai sauƙi ba mutum ya haɗu da abokansa a fili, musamman idan ba mutum ne mai son ya zauna a wuraren taruwa jama'a ba.

Padison na ba da shawarar mutum ya samu wasu ayyuka da rukunin mutane ke gudanarwa don ya haɗu da mutanen da suka dace da shi, yayin da shi kuma Hong ya ce ya shiga wani kulob ɗin unguwarsu.

"Amma ni ne mafi ƙarancin shekaru a cikinsu...ka ga kuwa ba zan haɗu da wasu mutane ba a haka".