Emery zai ci gaba da horar da Aston Villa zuwa 2027

An wallafa

Kociyan Aston Villa, Unai Emery ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da aiki a Villa Park har zuwa karshen kakar 2027.

Emery ya koma Villa Park cikin Nuwambar 2022 bayan korar Steven Gerrard, lokacin da kungiyar ke mataki na 16 a kasan teburin Premier League.

Mai shekara 52, ya ja ragamar kungiyar ta kare a mataki na bakwai a bara, hakan ya sa ta samu gurbin Europa Conference League, kuma na farko a gasar Turai tun 2010–11.

A kakar bana tana ta hudu a teburin Premier League, kuma daf take ta samu gurbin Champions League - ta bai wa Tottenham ta biyar tazarar maki shida, mai kwantan wasa biyu.

Villa za ta samu gagarumar ci gaba idan Emery ya lashe Europa Conference League, sannan idan kungiyar ta samu gurbin Champions League na badi.

Kawo yanzu Villa ta kawo karshen rade-radin da ake cewar watakila Bayern Munich ta yi zawarcin kociyan ko kuma Liverpool, wadanda masu horar da su za su bar aikin a karshen kakar nan.

A kwarewar da Emery keda ita ya kai Villa daf da karshe a Conference League, wadda za ta kara da Olympiakos da fatan kai wa zagayen karshe a gasar Turai a karon farko tun 1982.

Emery ya lashe Europa League uku tare da Sevilla, ya kuma dauki daya a Villarreal.

Ya horar da Arsenal wata 18, wadda ya kai Gunners mataki na biyar a teburin Premier League da kai wa wasan karshe a Europa League, inda Chelsea ta yi nasara.

Ya hada maki 115 a Premier League tun bayan da ya karbi aikin horar da Villa, kociyan da suke gabansa a wannan kwazon sun hada da na Manchester City da na Arsenal da kuma na Liverpool.