Hikayata 2023: Labarin Tsalle Ɗaya
An wallafa
Labarin Tsalle Ɗaya wanda Faridat Husain Mshelia da ke gida mai lamba biyu kan titin Catholic Church Road, a garin Suleja, jihar Naija ta rubuta, an gina shi a kan wata uwa mai ƙoƙarin nema wa 'ya'yanta maganin gyaran jiki.
Sai dai a ƙarshe ta yi nadama, bayan yin tsalle ɗayan da ya jefa ta cikin rijiya.
Bayan sanya ranar bikin 'yarta Jawaheer, sai ta shiga nema mata magungunan ni'ima da gyaran gado, to amma kash! Sai aka samu akasi inda aka dage bikin.
Wannan al'amarin ne ya jefa rayuwar Jawaheer cikin mummunan yanayi wanda ya sa uwar yin da-na-sani.









