Damuwar da masu shayarwa ke faɗawa, wadda mutane da dama ba su sani ba

..

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, By Fay Nurse
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A shekaru da dama, sabbin iyaye mata da suka haihu sun saba jin wannan kalmar da ke cewa "ruwon nono ya fi komai". A yayin da wannan kalmar ke karfafa muhimmancin shayarwa, kalamar iya haifar da matsin lamba ga iyaye mata da ke fuskantar kalubale wajen shayarwa.

Wasu matan na da burin su shayar da jariransu na tsawon lokaci amma kuma dalilai da dama su saka su yaye yaran da karfi da yaji.

Wadannan mata da dama sun tattauna da BBC kan kalubale da kunci da bakin cikin da suke ji biyo bayan yaye yaransu daga shan ruwan nono ko sun ƙi ko sun so saboda wasu dalilai ko da kuwa a ce lokacin yaye su yayi ko bai yi ba.

Jemma Munford zaune tana shan shayi

Asalin hoton, Alex Grace Photography

Bayanan hoto, Jemma Munford ta ce ta so shayar da jaririnta fiye da komai

Jemma Munford, wacce ta haifi danta Max a cikin shekarar 2017, ta shirya shayar da ɗanta ruwan nono zalla, amma kuma bayan kwana uku da fara shayarwa ta fara jin wahalar shayarwar.

"Ina zaune a kan kujera rike da jaririna, kawai na fashe da kuka kuma na kasa daina wa. " in ji Jemma.

Ta kwatanta makonni biyu da tayi tana shayarwa a matsayin "abu mai wahala da ban tsoro." Ta ce har abun ya kai ta hana mutane zuwa gidanta yayin da take ɓoye kanta a cikin daƙinta tana ƙoƙarin tabbatar da jaririnta ya iya kama nono.

Ta kara da cewa, shayarwa a gurinta abu ne mai ban gajiya da kuma kunya.

Jemma ta kuma ce jaririnta na da wata lalura inda fatarsa da ke haɗa harshensa da bakinsa ya matse sosai ba yadda ya kamata ba, wanda hakan ke bai wa yaron wahala sosai wajen kama nono.

Bayan wasu watanni, jaririntya ya fara ramewa wanda ke kuma nuna alamar dole sai sun koma asibiti, dalilin haka ne ya saka ta cire shi daga shan ruwan nono inda ta fara ba shi madarar yara.

Jemma na kallon hoton yaronta lokacin da yake jariri

Asalin hoton, Alex Grace Photography

Bayanan hoto, Jemma na kallon hoton yaronta lokacin da yake jariri

Jemma ta haifi jaririyarta ta biyu bayan shekara biyu kuma duk da cewa jaririyar ba ta da irin laluran yayanta Max, Jemma ta riga ta yanke shawarar ba za ta iya fuskantar shayar da ita ruwan nono na tsawon lokaci ba.

Amma kuma fa ta ce har yanzu, shawarar da ta yanke na damunta sosai.

"A mastayina na uwa, ban yi abubuwan da suka kamata nayi ba lokacin da ya kamata, kuma na ji kunƴar hakan matuƙa, kuma har yanzu ba na jin dadin abubuwan da na yi. " in ji ta.

Yanzu ta yi imanin cewa a lokacin tana fama da ƙunci da baƙin cikin bayar haihuwa duk da cewa ba a ayyana hakan a matsayin cuta ba a lokacin.

Mene ne ƙunci da baƙin ciki a lokacin shayarwa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Farfesa Amy Brown, mai bincike kan lafiyar jama'a, ta bayyana cewa bacin rai da ƙunci game da shayarwa ba wani sabbon abu bane, "Yawancin mata na yaye ƴaƴansu da wuri ba yadda suka shirya ba wanda hakan ke sa su ji kamar sunyi hasara wani abu."

Bincike ya nuna cewa mata suna son su shayar da ƴaƴnsua. A Burtaniya, kaso 81 na mata na shayar da yaransu nono zalla har zuwa wata shida amma hakan ya ragu zuwa kasa da kaso 26.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da shawarar shayar da jarirai nonon uwa zalla na tsawon watanni shida na farko rayuwarsu, domin yana matukar rage haɗurran da suka hada da mutuwar jarirai kwatsam (SIDS) da ciwon suga na yara da cututtukan zuciya, da kuma ƙiba, a cewar UNICEF.

A duniya baki daya, kaso 48 na jarirai ‘yan kasa da watanni shida yanzu ana shayar da su nonon uwa zalla, wanda ya karu da kashi 10 cikin 100 a cikin shekaru goma da suka gabata.

Kudancin Asiya ne ke kan gaba da kaso 60 cikin 100 na yawan shayar da jarirai nonon uwa zalla, sai Gabashi da Kudancin Afirka da kaso 58 sai Latin Amurka da Caribbean na da kashi 43 sai Afirka ta Yamma da ta Tsakiya na da kashi 40.

Gabashin Turai da Asiya ta Tsakiya kuma na da kashi 36, sai kuma Gabas da Arewacin Afirka na da kashi 35.

Deepti da yaronta na farko

Asalin hoton, Handout

Bayanan hoto, Deepti ta ce "Ba zan iya kwatanta adadin yadda nake son shayar da yarona ba, kullum cikin ɓacin rai nake."

Deepti, na ɗauke da cikinta na biyu wanda ya kai wata bakwai kuma tana fatan samun gogewa sosai kan shayarwa ba kamar lokacin da take shayar da yaraonta na farko ba.

A shekarar 2021, ta yi gwagwarmaya wajen shayar da danta nono sakamakon lalurar da fatarsa da ke haɗa harshensa da bakinsa ya matse sosai shima ba yadda ya kamata ba, wanda hakan ke bashi wahala sosai wajen kama nono wanda hakan ya sa ta riƙa tatse nonon a kwalba tana bai wa jaririnta

Amma duk da cewa yaron ya samu lafiyar lalurar, Deepti ta gwammace ta tatse nononta a kwalba ta bai wa yaron.

Deepti ta ce har yanzu tana nadamar rashin bai wa yoron nono ta hanyar ɗaura yaron a ƙafa ta sa ya kama kan nono.

Deepti da yaronta na farko

Asalin hoton, Handout

Bayanan hoto, Deepti da yaronta na farko

Me yesa iyaye mata suke dakatar da jariransu daga shan nono da wuri?

A yayin da Jemma da Deepti duk suka fuskanci kalubalen shayarwa saboda lalurar fatar yaransu da ke haɗa harshensu da bakinsa ya matse sosai ba yadda ya kamata ba, wanda hakan ya hana su kama nono, akwai sauran dalilai da dama da kan hana shayar da jariri yadda ya kamata.

Waɗannan matsalolin sun haɗa da ciwon nonuwa, tsagewar kan nonon uwa, ko zub da jini daga kan nanon uwa, saboda samar da madarar nono mai yawa ko kaɗan da dai sauransu.

Lisa Mandell daga kungiyar Ƙwararrun masu ba da gudunmawa kan shayar da nono wato (the International Lactation Consultant Association) tana ba da tallafi ga uwaye mata da ke fuskantar matsalolin shayarwa.

Ta jaddada mahimmancin samun shawarwari daga wajen kwararru da taimako da wuri-wuri.

"Idan mahaifiyar da ke da karancin madarar nono aka gano tana da matsalar thyroid, magance shi zai iya inganta samar da isashen ruwan nono," in ji ta.

Mandell ta kuma lura cewa bai kamata uwa da ji zafi wajen shayarwa ba, idan har tana jin zafi wajen shayarwa, to hakan na nuna cewa ba a daidai ta riƙe shi ba ko ba a daidai ya kama nonon ba.

Clare Murphy, darekta na Feed UK, ta jaddada cewa ciyar da jarirai abu ne mai muhimmanci da sarkakiya kuma ya kamata a tallafawa iyaye mata da nuna musu goyon baya ba tare da la'akari da yadda ko inda za su shayar da jariransu ba.

Deepti tana shirin sake gwada shayarwa amma ba za ta ƙara matsawa kanta ba in ji ta.