An ci Barcelona karo na biyu a La Liga a bana

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Sociedad ta doke Barcelona 1-0 a wasan mako na13 a La Liga da suka kara ranar Lahadi.

Sociedad ta ci ƙwallon ta hannun Becker tun kan hutu, haka suka koma zagaye na biyu har ta kai aka tashi daga karawar ba tare da Barcelona ta farke ba.

Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburi, amma da tazarar maki shida tsakani da Real Madrid ta biyu.

Ita kuwa Sociedad ta yi sama zuwa mataki na takwas da maki 18, bayan da suka yi fafatawar mako na 13.

Wannan shi ne karon farko da Sociedad ta yi nasara a kan Barcelona, wadda ta karɓi bakunci tun bayan ranar Asabar 9 ga watan Afirilun 2016 da ta ci 1--0 shima a gida.

Haka kuma shi ne karo na biyu da aka doke Barcelona a La Liga a bana daga karawa 13, tun bayan wanda Osasuna ta caskara ta 4-2 ranar 28 ga watan Satumba.

Wasa na uku da aka ci Barcelona kenan a dukkan karawa a kakar nan, bayan 2-1 da Monaco ta yi nasara ranar 19 ga watan Satumba a Faransa a Champions League.

Wasan da suka kara a bara a La Liga:

La Liga Litinin 13 ga watan Mayun 2024

  • Barcelona 2 - 0 Real Sociedad

La Liga Asabar 4 ga watan Nuwambar 2023

  • Real Sociedad 0 - 1 Barcelona

Wasa biyar da suka yi a baya a tsakaninsu Sociedad da Barcelona:

  • 13/05/24 (LIGA) Barça 2-0 Real Sociedad
  • 4/11/23 (LIGA) Real Sociedad 0-1 Barça
  • 20/05/23 (LIGA) Barça 1-2 Real Sociedad
  • 25/01/23 (LIGA) Barça 1-0 Real Sociedad
  • 21/08/22 (LIGA) Real Sociedad 1-4 Barça

Sociedad za ta je gidan Bilbao a wasan mako na 14 a La Liga ranar Asabar 24 ga watan Nuwamba, sai kuma ta karɓi bakuncin Ajax a Europa League ranar Alhamis 28 ga watan Nuwamba.

Ita kuwa Barcelona za ta je gidan Celta Vigo a La Liga ranar Asabar 23 ga watan Nuwamba, daga nan za ta karɓi bakuncin Stade Brest a Champions League ranar Talata 26 ga watan Nuwamba.