Yaya yiwuwar ɓarkewar yaƙi take a yankin Gabas ta Tsakiya?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 8

Yaƙin Gaza na ci gaba da kazancewa.

Isra'ila ta kai farmaki ta kasa a kudancin Lebanon, yayin da Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami kusan 200 zuwa Isra'ila. Isra'ilar ta kai harin bamabamai kan 'yan tawayen Houthi da ke Yemen.

Ci gaba da yaƙin da faɗaɗarsa zuwa wasu ƙasashe ya sanya 'yan siyasa a faɗin duniya na nuna damuwa da fargabar kada yakin ya mamaye yankin Gabas ta Tsakiya.

Mun tuntubi masu aiko wa BBC rahotanni daga yankunan da ake tashin hankalin, don jin ko akwai yiwuwar fadadar yakin har ya kasance na duniya baki daya.

Nawal Al-Maghafi, babbar mai bincike a sassan duniya kuma mai aiko da rahotonni

Kalmar "ana gab da fadawa bala'i" ita ake amfani da ita wajen bayyana halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.

An kashe sama da mutum 40,000 a Gaza, ga wasu sama da 2,000 a Lebanon cikin, ga ayyukan jin-kai da ke kara munana. Miliyoyin farar hula sun rasa muhallansu, garuruwa da kauyuka har da birane sun zama kufai. Wannan na daga cikin abin da ke tabbatar da ana kan wani siradi na barkewar bala'i mafi muni.

Muna ganin daya daga cikin mummunan tashin hankali, da bala'in da ba a taba gani ba cikin gomman shekaru.

A makon da ya wuce, Isra'ila ta yi gagarumin bikin murnar kisan shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah.

Mutuwar Nasrallah na Hezbollah da Isma'il Haniyeh na Hamas suka sanya Isra'ila jin dadi da samun 'yar gamsuwa, da ganin tamkar sun yi wa Iran yankan baya ne.

Babu shakka Isra'ila ta yi wa Hezbollah barna, yadda hare-hare ta sama suka dinga fadawa kan shugabannni da masu karfin fada a ji na kungiyar.

Shekara guda da aka kwashe ana yaki a Gaza, ya daidaita miliyoyin farar hula.

Ana ganin hakan ya yi wa kungiyar Hamas illah, sai dai babu alamun kawo karshen Hamas ko dai a matakin siyasa ko na soji.

Kisan Nasrallah da martanin da Iran ta maida ya sanya yankin baki daya kan tsinin yiwuwar barkewar yaki.

Kalaman shugabannin Isra'ila bayan harin na Iran, na nuna suna da aniyar mayar da martanin da ka iya jefa yankin cikin hadari, kuma kasashen yankin ne a sahun gaba.

Na farko dai ita Iran din kan ta wadda ke mara wa Lebanon baya da Syria da Yemen da kuma Iraqi, sai kuma lamarin ka iya shafar Isra'ila da kawayenta kamar Amurka da Birtaniya.

Abin tambayar a nan shi ne, ta yaya Isra'ila za ta mayar da martani?

“Wannan wata babbar dama ce cikin shekaru 50 a sauya yadda ake kallon Gabas ta Tsakiya,” in ji tsohon Firaministan Isra'ila Naftali Bennett a sakon da ya wallafa a shafinsa na X.

Ya ce "kamata ya yi Isra'ila ta kai hari Iran don lalata cibiyoyin makaman nukiliyarta, domin karya lagon gwamnatin 'yan ta'adda”. idan har kalamansa na nuna ita ce aniyar hukumomin kasar, za mu iya cewa muna gab da ganin wani yanayi na rashin tabbas da zai daidaita yankin.

Nisrine Hatoum, wakiliyar sashen Larabci na BBC, a birnin Beirut

'Yan Lebanon ba su son a yi fito na fito a gwabza yaki.

Tabbas fargaba na karuwa a kasasshe makofta ciki har da Syria da Iraƙi da Iran da Yemen, watakil har da Jordan. Fargabar ta rubanya tun bayan hare-haren makamai masu linzamin da Iran ta yi zuwa Isra'ila, akwai alamun karin wasu hare-haren nan da kwanaki masu zuwa.

Kuma idan Iran ta kara kai wa Isra'ila hari, Amirka da kasashen yamma da ke marawa Isra'ilar baya za su shiga lamarin, hakan ka iya sauya yadda ake yakin.

Isra'ila dai aniyarta ita ce murkushe Hezbollah da mayakanta a Lebanon, ba wai sojin kasar ne a gabanta ba.

Abin da jami'an Lebanon za su iya yi, shi ne kare yaduwar yakin.

Jami'ai a Lebanon na aiki tukuru da amfani da diflomasiyya bisa jagorancin Faransa domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

Duk kokarin da ake yi ana son amfani da kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701, da zai karfafa da taimakawa sojojin Lebanon da girke wasu a kudancin kasar.

A Lebanon mutane sam ba sa son Yaki, ko tashin hankali musamman ganin abin da ya faru a watan Oktobar shekarar 2019.

Mutane da dama na son zaman lafiya da kaucewa tashin hankalin. Wasu 'yan Lebanon sun yi amanna da cewa an janyo su cikin yakin ne ta karfi da yaji, ba su san hawa ba bare sauka, dan haka yakin nan ba na su bane.

To amma za a iya kaucewa yaduwar yakin nan nbe kawai idan an yi amfani da kokarin diflomasiyya domin kawo karshen yakin.

Idan mukai waiwaye zuwa shekarar 2006, yakin da Isra'ila ta kwashe kwanaki 34 ta na gwabzawa, lamari ne da ya sha banban da na yanzu. A lokacin babu yaki a Gaza, bare ace Syria da Iraqi da Iran da Yemen sun tsoma baki.

Kuma kar mu manta da a yakin na shekarar 2006, akwai kasashen yankin da dama da suka tsoma baki. Amma idan mukai duba ga ita kan ta Lebanon a matsayin kasa, mai rauni ce, da sojojin da ba za su iya daukar matakin azo a gani ba.

Muhannad Tutunji, wakilin sashen Larabci na BBC a birnin Kudus

Yankin gabas ta tsakiya ta ga abubuwa da dama da ka iya tada yaki a yankin da duniya. Ci gaba da yaki tsakanin Hezbollah da Isra'ila ko ma Iran na sanya fargabar barkewar yaki.

Duk da lamuran da suka faru a baya-bayan nan kamar kisan shugaban Hamas Isma'il Haniyeh da kisan shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah da manyan jami'an kungiyoyin biyu ta fuskar siyasa da soji, ya sake karfafa masu hasashen barkewar yaki a yankin.

A matsayina na dan jarida da ke bibiyarharkokin Isra'ila da tarihin karawarsu da Hezbollah, mu na zargin kisan da Isra'ila ta yi wa Nasrallah ka iya janyo Iran cikin yakin.

To amma hakan bai faru ba.

Manyan masu fada a ji a yanki na taka rawa wajen tabbatar da lamura ba su lalace ba, da kuma rawar da Amirka ke takawa kan hakan.

Duk inda za a je a zo dai, maganar guda daya ce kaucewa yaduywar yakina yankin na gabas ta tsakiya.

Amirka ta yi nasarar shawo kan lamarin. A wancan lokacin, mun kawo mu ku rahoton an yi tattaunawa tsakanin shugaban Amirka Joe Biden da firai ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ta wayar tarho, domin tausasar zukata jim kadan bayan kai harin da aka kai da akalla makamai masu linzami da ke cin dogon zangoi har kusan 100.

A lokacin da shugabannin biyu sun tattauna akan yadda za a sassauta wasu abubuwan da yadda za a rage barnar yakin. Amirka ta kuma bayyana ba za ta hada kai da Isra'ila wajen kai harin ba.

A lokacin da muka kawo mu ku wannan rahoton, Amirka ta yi rawar gani wajen Martanin da Isra'ila ta maida kamar yadda jami'ai suka bayyana mai karfi ne, da ke kara karfafa yiwuwar dagulewar lamura.

Kuma wannan ita ce aniyar Isra'ila tuntuni.

Firaminista Netanyahu na son sauya Gabas ta Tsakiya, ya yi amanna abu ne mai bkamar wuya idan bai kassara Iran ba, wadda Isra'ila ta ce tamkar ''an kashe maciji ba a sare kai ba.''

Abin tambayar shi ne: ko Amurka za ta nade hannu ta bar Isra'ila ta aikata hakan?

Eman Eriqat, wakiliyar sashen Larabci na BBC, mai aiko da rahotanni daga yankunan Falasdinawa

Farin ciki da tsoro: wannan shi ne halin da Falasdinawa suka samu kan su a ciki a ranar Talata, daren da Iran ta kaddamar da harin makamai masu linzami kusan 200 zuwa Isra'ila.

Yawancin Falasdinawa sun jima suna jiran wannan lokaci tun barkewar yakin Gaza. Sun yi amanna da taimakon kasasshen waje zai karfafa gwiwar al'umar Gaza da Faladinawa baki daya.

Wurin da makamin Iran ya fada ya kasance kusa da inda Falasdinawa suke, hakan ya ba su damar zuwa daukar hoton tarihi.

Kisan shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah da kisan Isma'il Haniyeh na Hamas a watan Yuli sun kara fadada yiwuwar yakin nan.

Yanayin da ake ciki a halin yanzu ya yi kama da wanda aka gani shekarun baya, inda Falasdinawa ke kwatantashi da ranar Intifada, ko wadanda suka ga mummunar ranar 'Nakba'' a shekarar 1948 sun ce tabbas tarihi ya maimaita kan shi.

Shekara da shekaru, hukumomin Falasdinu sun mai da hankali akan bubuwan kamar haka:

  • Muhimmancin amfani da matakin siyasa wajen dakatar da ayyukan soji.
  • Karkata daga tashin hankali zuwa amfani da damar na kafa kasashe biyu masu cin gashin kai.

Sun yi amanna wannan zai bai wa Falasdinawa kafa kasarsu a shekarar 1967 da iyakar Isra'ila.

Tun ranar 7 ga watan Oktoba 2023, lokavcin da aka fara yakin Gaza, shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya yui kira ga kasasshen duniya su shiga batun domin gaggauta dakatar da bude wuta.

Duk da kiran na shi ya samu karbuwa, amma ba a daina kai hare-hare tsakanin sojin Isra'ila da na Hamas.

Kasra Naji, wakiliyar sashen Fasha na BBC

Madakin kai wa Isra'ila hari kai tsaye daga Iran, ba abu ne mai sauki ba, kuma ba mataki ne da jagoran addini Ayatollah Ali Khamenei ya dauka da sauki na.

Bai cika ba da umarni da daukar mataki cikin gaggawa irin hakja ba. Ya fi son daukar matakin hakuri, da shiryawa kafin maida martani.

Amma shi da gwamnatinsa na fuskantar matsin lamba daga cikin mutanensu da suka fi tsauri, da mayakan da ke yankin, da kuma muhimmancin maida martani cikin gaggawa kan kisan shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah.

Sun kuma kara matsa lamba kan maida martanin kisan da aka yi wa kwamandan Hezbollah a kudancin Lebanon.

Iran ta shiga yanayi na jin kunya, musamman da ta gagara maida martani kan kisan da aka yi wa shugaban kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh a birnin Tehran a watan Yuli.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, shugabannin Iran sun sani sarai ba su shirya tada yaki a wannan lokacin ba.Ta fuskar soji, Iran ta san ba ta kama kafar Isra'ila ba, wadda ta ke da karfi ta kowacce fuska indai ta fannin soji ne da Isra'ila.

Sararin samaniyar Iran wuri ne da Isra'ila ta ke zuruftu a duk lokacin da ta ga dama.Ta fuskar tattalin arziki Iran na fama da tarin takunkumai da Amirka ta lafta ma ta.

Ta fuskar siyasa kuma a iya cewa 'yan kasar Iran ba su wani waye kan hakan ba.Dan haka idan yaki ya taso, daidaikun 'yan kasar ne za su bada goyon baya kan hakan, sakamakon kasar na fama da na ta matsalolin na cikin gida. Iraniyawa sun yi amanna shuiga yaki na nufin a kara laftawa kasar takunkuman karya tattalin arziki, da zai kara jefa su cikin matsin rayuwa. Yawanci dai ba ma sa yi wa Isra'ila kallon abokiyar gaba ko makiyiya.

Amma duk da haka, jagoran addinin dole da ya yi wata kasada, da fatan hare-hare kan sojoji da wurare ka iya yin abin nan na 'a tauna tsakuwa, domin aya ta ji tsoro', kuma ta hakan Iran din za ta iya kai labari.