Wolves na zawarcin Ramsdale, Juventus na son Sterling.

Aaron Ramsdale

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Aaron Ramsdale
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wolves ta gabatar da wani kuduri ga Arsenal domin ta ba ta aron mai tsaron ragarta da kuma Ingila Aaron Ramsdale kuma za ta iya siyansa a bazarar badi. (Athletic - subscription required), external

Juventus na zawarcin dan wasa mai kai hari na Chelsea da Ingila Raheem Sterling mai shekara 29, yayin da akwai rashin tabbas game da makomarsa a kungiyar ta Chelsea. (Mail), external

Ita ma Kungiyar Al-Hilal ta Saudi Pro League na zawarcin dan wasa mai tsaron bayan Manchester City da Ingila Kyle Walker da kuma dan wasan baya na Portugal Joao Cancelo. (Guardian), external

Manchester City na son ta sake siyan dan wasan tsakiyar Jamus Ilkay Gundogan mai shekara 33, daga Barcelona. (Athletic - subscription required), external

Real Sociedad ta ki ta rage farashin da ta sanyawa dan wasan tsakiyar Sfaniya wanda Arsenal ke sha’awarsa watau Mikel Merino mai shekara 28. (Mirror), external

Brentford na fatan dan wasa mai kai hari na Ingila Ivan Toney zai koma taka leda a Al-Ahli ta Saudi Pro League kuma ta na fatan samun kudi kusan fam miliyan hamsin (Times - subscription required)

Sai dai ita ma Chelsea na sha'awar Toney. (Sun)

Fulham na tunanin ko ta koma Crystal Palace da wani sabon tayi kan dan wasa mai tsaron bayan Denmark Joachim Andersen mai shekara 28 . (Sky Sports), external

Ita ma Fulham ta fara shirin sake tayin dan wasan tsakiyar Manchester United da Scotland a karo na uku, Scott McTominay mai shekara 27. (Teamtalk), external

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Arsenal ta yi watsi da tayin fam miliyan 25 da Nottingham Forest ta yi wa dan wasan gaba Eddie Nketiah mai shekara 23 . (Sun), external

Kawo yanzu Newcastle ta yi ammanar cewa za ta iya siyan dan wasa mai tsaron bayan Ingila Marc Guehi, mai shekara 24 daga Crystal Palace, Sai dai kuma tana nazari kan dan wasa mai tsaron bayan Liverpool da Ingila Joe Gomez, mai shekara 27, tare da dan wasan tsakiyar baya na Chelsea da Ingila Trevoh Chalobah mai shekara 25. (i Sport), external

Manchester United za ta jira har zuwa ranar karshe ta cinikin 'yan wasa don siyan Manuel Ugarte, mai shekara 23, tare da fatan Paris St-Germain za ta rage farashin dan wasan tsakiyar Uruguay na fan miliyan 51. (Guardian), external

Aston Villa da Real Betis da kuma Roma na zawarcin dan wasan tsakiyar Tottenham da Argentina, Giovani Lo Celso, mai shekara 28,. (Express), external

Everton ta yi tambaya game da batun biyan Yuro miliyan 60 domin siyan dan wasan gaban Atletico Mineiro da kuma Brazil, Alisson Santana, mai shekara 18.(Globo - in Portuguese), external

Nottingham Forest na duba yiwuwar sake tuntubar Feyenoord akan dan wasanta mai kai mata hari da kuma Mexico Santiago Gimenez, mai shekara 23, bayan da aka yi watsi da tayinta na yuro miliyan 25. (Athletic - subscription required), external

Wolves na zawarcin dan wasan tsakiyar baya na Sheffield United da Bosnia Herzegovina Anel Ahmedhodzic, mai shekara 25. (Football Insider), external

Chelsea ta sanar da Napoli cewa ta na son kudi akalla yuro miliyan 40 kan dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku,mai shekara 31, yayin da Blues ke shirin yin watsi da tayin kudi na yuro miliyan 30 daga kungiyar ta Italiya . (Ben Jacobs), external

Dan wasa mai tsaron bayan Chelsea da Ingila a tawagar masu shekaru kasa da 21 Bashir Humphreys, mai shekara 21, na gab da komawa Burnley a matsayin aro wanda kuma aka bata damar siyansa idan tana so. (Athletic - subscription required), external

Dan wasa mai tsaron bayan Burnley da Brazil Vintinho, mai shekara 25, ya amince ya koma kungiyar Botafogo ta kasar Brazil. (Globo - in Portuguese), external