Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An tuhumi Bentancur da amfani da kalaman ƙiyayya
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta tuhumi ɗan wasan tsakiya na Tottenham, Rodrigo Bentancur, bisa zarginsa da yin amfani da kalaman wariya kan abokin wasansa Son Heung-min.
Bentancur dai ya yi kalaman ne wata hira da ya yi da wani gidan talabijin a Uruguay a watan Juni, inda aka yi masa tambaya kan ƙyaftin ɗinsa Son, inda ya ce: "Sonny? Yana ma iya zama ɗan uwan Sonny saboda ai duk kamarsu ɗaya.''
Daga baya dai Bentancur ya nemi afuwa a shafinsa na Instagram kuma ya ce bai furta kalaman da niyyan ɓatanci ba.
Hukumar ta FA ta ce an tuhumi ɗan wasan na Uruguay mai shekaru 27 da laifin keta ƙa'idar FA ta E3 da ta jiɓanci rashin da'a dangane da hira da manema labarai.
Ɗan wasan dai na iya fuskantar dakatarwa daga buga wasanni shida zuwa goma sha biyu idan har aka same shi da laifi.
Bentancur yana da har zuwa ranar Alhamis, 19 ga Satumba don amsa tuhumar.