Kocin Wolves ya ce ba zai sauya tunaninsa ba har sai ya samu nasara

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Wolves Gary O'Neil ya dage kan cewa "tunaninsa ba zai sauya ba" duk da matsin lambar da yake ciki bayan rashin ƙoƙarin da yake yi tun farkon kakar 2024-25.

Magoya bayan da suka je kallon wasa sun riƙa waƙe cewa "da safe za a kore ka" a wasan da ƙungiyar ta O'Neil ta yi rashin nasara da ci 4-0 a hannun Everton.

Rashin nasarar da ta yi a Goodison Park shi ne na tara a Premier yayin da ta yi nasara a wasa biyu kacal kuma tana matsayi na 19 a tebuti da maki tara kacal a wasa 14 da aka yi.

Duk da koma bayan da yake samu, Wolves ta samu maki bakwai ne a watan Nuwamba ta yi rashin nasara biyu da canjaras ɗaya, abin da ya sa aka sanya sunan O'Neil a cikin koci mafiya kwazo a watan.

"Zan ci gaba da nawa ƙoƙarin har sai abubuwa sun sauya," in ji O'Neil.

"Na jagoranci atisaye a yau, kuma duka ciki za ka ga babu wanda ya kai ni dagewa da kuma nuna kwarewa.

"Suka na cikin wani ɓangaren aikin. Watakila mako biyu da suka gabata da muka ci kwallo huɗu a wasan Fulham kowa yana murna ana tafi, amma lokacin da abubuwa ba su yi kyau ba akwai buƙatar ka tashi tsaye. Tunanina ba zai sauya ba, ko da yaushe zan ci gaba da kallon yadda za mu yi nasara."

Wolves ta gaza ci ko wasa guda daga cikin 10 na farko da ta buga a wannan kakar, ta kuma yi nasararta ta farko ne a rabar 9 ga watan Nuwamba - Inda ta doke Southampton 2-0 a gida.

Sai nasarar da suka yi a Fulham 4-1 da ta biyo baya, amma rashin nasara a hannun Bournmouth da Everton ta dakatar da nasarar da Wolves ta fara samu.

Wolves za ta je wasa na 14 a West Ham ranar Litinin, yayin da shi me kocin Julen Lopetegui wanda O'Neil ya maye gurbinsa a Wolves shi ma na cikin matsijn lamba.