Na shirya tsaf don shiga sabuwar rayuwa a Man United - Rashford

Marcus Rashford

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marcus Rashford made his debut for Manchester United in 2016
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗanwasan gaba na Manchester United Marcus Rashford ya ce "a shirye yake" game da fuskantar sabon ƙaluble a sana'arsa ta ƙwallon ƙafa a ƙungiyar.

An ajiye Rashford mai shekara 27 daga cikin tawagar ƙungiyar yayin wasan hamayya tsakaninsu Manchester City ranar Lahadi.

Sabon koci Ruben Amorim ya tabbatar cewa ba wata matsala ba ce ta sa ya yi hakan, amma ya nuna alamun yana son ɗanwasan Ingilan ya ƙara ƙoƙari a fili da kuma wajen filin.

Yayin wata hira da marubucin labarin wasanni Henry Winter a dandalin X, Rashford ya ce: "Idan na san lamari ya riga ya lalace ba zan so na sake munana shi ba. Na ga irin yadda wasu 'yanwasan suka bar kulob ɗin, saboda haka ba ni son na yi haka ni ma.

"Idan zan bari zan fitar da sanarwa, kuma ni ne zan sanar da hakan. Idan zan tafi 'ba zan ƙullaci kowa ba'. Ba zan ci mutuncin Man United ba. Haka nake ni.

"Ina ganin na shirya tsaf don fuskantar sabon ƙalubale da kuma sabuwar rayuwa nan gaba."

Rashford ya ci wa Man United ƙwallo 138 cikin wasa 426 tun bayan da ya fara taka mata leda a 2016, bayan ya shiga babbar ƙungiyar daga ta matasa.

Kakar 2022-23 ce mafi albarka a rayuwarsa, inda ya ci ƙwallo 30 a dukkanin gasa.

Sai dai kuma yana fama tun daga wata 18 zuwa yanzu, abin da ya sa ake yawan sukarsa.