Lookman zai bar Atlanta, Man City na son Wirtz

Ademola Lookman

Asalin hoton, PA Media

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City na son ɗan wasan tsakiya na Jamus mai taka leda a Bayer Leverkusen, Florian Wirtz, 21, yayin da ta ke tunanin sallamar ɗan wasan tsakiya na Ingila James McAtee, mai shekara 22. (Mail)

Watakil Newcastle za ta bari mai kai hari na Sweden, Alexander Isak ya bar ƙungiyar, idan ba ta samu gurbi a gasar Champions League na kaka mai zuwa ba, ya yin da ƙungiyoyin Liverpool da Arsenal ke sha'awar ɗan wasan mai shekara 25. (Mirror)

Mai kai hari na Najeriya Ademola Lookman, 27, zai bar Atalanta bayan rashin jituwa da manaja Gian Piero Gasperini. (Sky Sports Switzerland)

Newcastle ta nuna sha'awar ɗaukar Lookman, sai dai za ta iya fuskantar ƙalubale daga Manchester United wanda ita ma ke zawarcin ɗan wasan. (Teamtalk)

Ɗan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, 31, wanda ya bar Juventus a watan Nuwamban da ya gabata, zai iya komawa taka leda a Inter Miami idan dakatarwar da aka yi masa kan shan kwayoyin ƙara kuzari ta ƙare a watan Gobe, bayan ya gana da David Beckham. (Manchester Evening News)

Ɗan wasan tsakiya na Belgium, Kevin de Bruyne na jira ya ga ko har yanzu Manchester City na son tsawaita kwantiraginsa, idan ya samu tabbacin haka, ɗan wasan mai shekara 33 ya amince ba zai ba zai buga wasanni da dama ba idan aka ƙulla sabuwar yarjejeniya da kulob ɗin. (Mirror)

Dan wasan tsakiya na Croatia Luka Modric, 39, zai ci gaba da zama a Real Madrid har lokacin da ya ga damar barin ƙungiyar, kamar yadda koci Carlo Ancelotti ya tabbatar masa. (Fabrizio Romano)

Real Madrid na tattaunawa kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Netherlands Vigil van Dijik mai shekara 33, wanda kwantiraginsa da Liverpool zai kare a bazara mai zuwa. (Marca)