Wirtz ya zama matashin da ya ci kwallo a Bundesliga

Florian Wirtz

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Florian Wirtz ya zama matashin dan wasa da ya zura kwallo a raga a gasar Bundesliga, bayan da ya ci Bayern Munich a wasan mako na 30 ranar Asabar.

Bayern Leversusen ta karbi bakuncin Bayern Munich ta kuma sha kashi a gida da ci 4-2.

Wadanda suka ci wa Bayern kwallayen sun hada Kingsley Coman da Leon Goretzka da kuma Serge Gnabry tun kan hutu, bayan da Lucas Alario ya fara ci wa Leverkusen.

Matashin dan kwallon ya shiga karawar daga baya, kuma a minti na 89 ya samu kwallo ya zura a ragar Munich inda Manuel Neuer yana kallo ya kasa tsare ragar.

Wirtz ya fara taka leda a matashin dan wasan kungiyar Colone daga baya ne ya koma Leverkusen a 2020, kuma kwallon farko kenan da ya ci wa kungiyar.

Dan wasan tawagar matasan Jamus ya ci kwallo yana da shekara 17 da kwana 34, inda ya doke tarihin da dan wasan Borussia Dortmund, Nurin Sahin ya kafa da ya ci kwallo a 2005 yana da shekara 17 da kwana 82.

Bayern Munich ta ci gaba da jan ragamar teburin gasar Jamus, kuma tana harin lashe kofin Bundesliga na takwas a jere.

Kungiyar da Hans Flick ke jan ragama ta yi rashin nasara a wasa daya tal daga 21 a baya a dukkan fafatawa a bana, tana da maki 70 a wasa 30 da ta buga a shekarar nan.

Bayern ta yi rashin nasara a wasa biyu daga 26 da ta buga tun lokacin da Flick ya maye gurbin Niko Kovac wanda aka kora a cikin watan Nuwamba.

A kuma ranar Laraba Bayern za ta buga wasan daf da karshe a kofin kalubalen Jamus da Eintracht Frankfurt ranar Laraba.