Sama da rabin manyan mutane na duniya za su yi teɓa nan da 2050 - Rahoto

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Sama da rabin manyan mutane a duniya da kuma kashi ɗaya cikin uku na yara ne aka yi ƙiyasin za su yi ƙibar da ta wuce ƙima ko kuma su yi teɓa nan da shekara ta 2050.

Sabbin alƙaluman na ƙunshe ne cikin wani bincike da aka wallafa a mujallar The Lancet da ya karaɗe sama da ƙasashe 200.

Masu binciken sun yi gargaɗin cewa ƙaruwar teɓa za ta hauhawa cikin sauri a ƙarshen shekaru goman da muke ciki, musamman a ƙasashe masu ƙarancin arziki.

Sai dai kuma, ƙwararru na cewa idan gwamnatoci suka ɗauki matakan gaggawa yanzu, akwai damar kare "aukuwar bala'i".

Zuwa 2021, kusan rabin al'ummar duniya da suka mallaki hankalinsu - maza biliyan ɗaya da mata biliyan 1.11 masu shekara 25 ko fiye - za su lukutaye.

Adadin masu wannan larura a cikin maza da mata ya ninka tun daga shekarun 1990.

Idan abin ya ci gaba a haka, masu kamuwa da larurar a cikin manya za su ƙaru zuwa kashi 57.4 cikin 100 a maza da 60.3 a mata zuwa 2050.

Game da yawan mutanen, China (miliyan 627), da Indiya (miliyan 450), da Amurka (miliyan 214) za su zama ƙasashen da suka fi yawan masu ƙiba fiye da kima a 2050.

Sai dai, ƙaruwar al'ummar na nufin masu binciken na hasashen samun ninki biyu da rabi na masu ƙibar a ƙasashen kudu da hamadar Sahara zuwa miliyan 522.

Najeriya kaɗai, za ta samu sama da ninki uku - daga miliyan 36.6 a 2021 zuwa 141 a 2050. Hakan zai sa ta zama ƙasa ta huɗu mafi yawan manya masu ƙiba fiye da kima.

Marubutan binciken sun aminta cewa bincikensu bai duba irin tasirin da magungunan rage ƙiba za su yi ba - kuma za su iya taka muhimmiyar rawa nan gaba.

Ƙwararru na cewa idan gwamnatoci suka ɗauki matakan gaggawa za a iya kare mutanen da ke cikin haɗari.

Farfesa Emmanuela Gakidou ce ta jagoranci binciken a cibiyar Health Metrics and Evaluation (IHME) da ke Jami'ar Washington ta Amurka.

Ta ce: "Gwamnatoci za su iya yin amfani da hasashenmu na kowace ƙasa game da matakai, da lokaci, da hanzarin sauyin da muka hasaso game da ƙiba domin gano abin da ya kamata su saka a gaba, musamman al'ummomin da suka fi buƙatar tallafi da wadanda za su fi yin ƙibar.

"Matsalar da ba a saba gani ta ƙiba fiye da kima annoba ce da kuma gazawar al'umma baki ɗaya," kamar yadda ta bayyana.

Maganar ƙiba fiye da kima na ƙaruwa musamman a tsakanin yara ƙanana.

Adadin ƙaruwar masu ƙibar a tsakanin yara da matasa (daga kashi 8.8 zuwa 18.1 cikin 100) da baligai masu ƙananan shekaru ('yan ƙasa da shekara 25 - daga kashi 9.9 zuwa 20.3) sun ninka a tsakanin 1990 da 2021.

Sai dai, zuwa 2050 ɗaya cikin uku na yara zai fuskanci matsalar.

Ɗaya daga cikin jagororin marubutan, Dr Jessica Kerr ta cibiyar lafiya ta Murdoch Children's Research Institute a Australia, ta ce adadin na nuna ƙalubale ga ɓangaren lafiya a shekaru masu zuwa.

"AMma idan muka ɗauki matakai yanzu, daƙile aukawa cikin ƙiba fiye da kima a ɓangaren yara da maya abu ne mai yiwuwa," in ji ta.

"Hasashenmu ya gano yara da manya a mafi yawan ƙasashen Turai da kudancin Asiya da raye cikin ƙiba mai yawa, waɗanda suka kamata a kula da su.

"Mun kuma gano mutane da yawa, musamman mata manya, a Amurka ta Arewa, da Australasia, da Oceania, da Afirka ta Arewa, da Gabas ta Tsakiya, da Latin Amurka da ake tunanin za su samu ƙiba fiye da kima.

"Wannan abu ne mai muhimmanci idan muna son mu guje wa ƙiba fiye da kima da kuma gagarumar matsalar lafiya a al'umma mai zuwa."