Waiwaye: Zawarcin da APC ke yi wa NNPP a Kano da barazanar IMPAN na rufe gidajen mai

.

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Abdullahi Ganduje shugaban APC na ƙasa da Rabi'u Kwankwaso jagoran NNPP
An wallafa

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman labaran da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

A makon da ya gabata ne jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shiga zawarcin kananan jam'iyyun adawa ciki harda NNPP ta Rabi'u Musa Kwanwkaso da mabiyansa.

Shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya shaida wa BBC cewa tuni suka aike da goron gayyata ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da jagoran jam'iyyar NNPP na kasa Rabiu Musa Kwankwaso.

Ganduje ya yi waɗannan kalamai ne a wani taro da ya jagoranta da shugabannin jam'iyyarsa ta APC a jihar Kano, inda ya ce dama can uwa ɗaya uba ɗaya suke da su Kwankwason.

Tun da farko rahotonni sun ce shugaban ƙasar ne Bola Tinubu ya umarci jagororin jam'iyyar APC na Kano da su sulhunta da jam'iyyar NNPP a Kano.

Atiku ya nemi gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan bashin dala biliyan 3.3 da NNPC ya ciyo

.

Asalin hoton, X/Atiku Abubakar

A tsakiyar makon da ya gabatan ne kuma jagoran adawar Najeriya Atiku Abubakar ya ce ya kamata gwamnatin shugaba Tinubu ta fito ta yi wa 'yan Najeriya bayani kan bashin dala biliyan 3.3 da kamfanin mai na ƙasar NNPC ta ciyo da nufin farfaɗo da darajar kudin ƙasar.

A shekarar da ta gabata ne Kamfanin mai na ƙasar NNPC ciyo bashin domin taimakawa wajen farfaɗo da darajar naira a kasuwar musayar kuɗaɗe.

To sai dai a cikin wata sanarwar da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fitar, ya ce wani abin mamaki shi ne har yanzu gwamnati ba ta ce komai ba game da lamarin, kuma bayanan kawai da ake samu kan batun, ana samun su ne ta wasu majiyoyin da ba na hukuma ba daga kamfanin.

Farashin shinkafa ya ƙaru da kashi 81 a 2023 - NBS

.

Asalin hoton, Getty Images

A cikin makon ne kuma wani rahoto da hukumar ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta fitar ya ce an samu tashin farashin shinkafa da kashi 81 cikin 100 a cikin shekarar guda a ƙasar a shekarar 2023.

NBS ta ce farashin kilogiram ɗaya na shinkafa 'yar gida ya ƙaru da naira 411.76 idan aka kwatanta da 506 da aka sayar da ita a watan Disamban 2022.

Cikin rahoton farashin wasu kayyaki a watan Disamban 2023, da hukumar ta fitar ranar Laraba ya nuna cewwa matsakaicin farashin kilo guda na shinkafar gida a watan Disamban 2023 shi ne naira 917.93.

Muna daf da rufe gidajen manmu - IPMAN

.

Asalin hoton, Getty Images

Haka kuma a makon da muke bankwanan da shi ne ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya, (IPMAN), ta koka game da wasu matsaloli da dama da 'ya'yanta ke fuskanta wajen samun man da suke sara daga kamfanin mai na ƙasar (NNPCL) don kai wa gidajen mansu musamman na yankin arewacin ƙasar.

Ƙungiyar ta ce wannan lamarin yana iya haifar da ƙarancin man har da ma rufe gidajen mai da dama.

Mataimakin shugaban ƙungiyar, Zarma Mustapha, ya shaida wa BBC cewa mafi yawan lokaci man fetur ɗin da suke samu daga NNPCL ba ya kai yawan da suke buƙata lamarin da ya sa suke siyan mai daga depo-depo masu zaman kansu kuma galibi sukan sayi man ne a kan farashi mai tsada wanda yake tasiri kan farashin da suke siyar da man a giajen mansu.