Hotunan yadda aka bayar da lambar yabo ga zaratan mawaƙan duniya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

A daren Litinin ne aka gudanar da bikin bayar da lambar yabo ga mawaƙan duniya na shekara ta 2025.

An gudanar da bikin ne a Los Angeles, da ke jihar California na ƙasar Amurka, birnin da ya yi fama da gobarar daji a baya-bayan nan.

Mawaƙiya ƴar Najeriya Tems, wato Temilade Openiyi ta lashe lambar yabo a bikin, inda yanzu ta sha gaban sauran takwarorinta mawaƙa na Najeriya wajen samun irin wannan kyauta.

Sai dai mawaƙiyar Amurka, Beyoncé ce ta fi ɗaukar hankali, inda kundin jerin waƙoƙinta mai taken 'Cowboy Carter' ya lashe kundi mafi shahara a duniya.

Wannan ce lambar yabon Grammy ta 67 da Benyonce ta lashe a tarihi.

Lokacin da aka ambaci sunanta kundin waƙoƙin nata a matsayin wanda ya yi zarra, Benyonce ta rungume ɗiyarta Blue Ivy da kuma mijinta Jay-Z kafin hawa kan dandamali domin karɓar kyautar.

A yanzu mawaƙiya Tems ta sha gaban mawaƙa irin su Davido da Burna Boy wajen lashe kyautar ta Grammys.

Mawaƙa Kendrick Lamar da Dave Free sun lashe kyautar bidiyon waƙa mafi ƙayatarwa a waƙarsu ta 'Not Like Us".