An ci tarar Arsenal saboda jan katin da aka yi wa Lewis-Skelly

Premier

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon kafa ta Ingila ta ci tarar Arsenal £65,000, saboda kasa tsawatarwa ƴan wasa, bayan korar Myles Lewis-Skelly a wasan Premier League da Wolverhampton.

Hukumar ta ci tarar Gunners saboda ƴan wasa sun yanyame alkalin wasa da cewar ''ba su nuna halin da'a ba'' ranar 25 ga watan Janairu a Molineux.

Ƴan wasan Arsenal sun zagaye alkalin wasa Michael Oliver a lamarin da ya faru a minti na 43, bayan da aka bai wa Lewis-Skelly jan kati kai tsaye, saboda ketar da ya yi wa Matt Doherty.

Mai kula da VAR, Darren England ya jaddada hukuncin rafli, Oliver da cewar Lewis-Skelly ya yi keta mai muni.

Arsenal ta ɗaukaka kara kan dakatar da matashin mai shekara 18 daga buga wasa uku daga baya aka soke hukuncin.

Bayan kammala karawar wani kwamitin kwararrun jami'ai ne suka yi bitar wasan, sun kuma ce jami'an tsaro na bincike kan barazanar da aka yi wa Oliver da shi da iyalansa a kafar sada zumunta.

Arsenal tana mataki na biyu a teburin Premier League da tazarar maki bakwai tsakani da Liverpool mai jn ragama.