Haaland ya nutsar da Everton cikin ƴan ukun karshe a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Erling Haaland ya ci ƙwallon farko a Premier tun bayan cikin watan Nuwamba, hakan ya sa Manchester City ta samu maki uku a kan Everton.
City ta karbi bakuncin Everton ne a wasan mako na 23 a babbar gasat tamaula ta Ingila a Etihad ranar Lahadi, inda Haaland ya zura biyu a raga.
Ɗan kasar Norway ya koma wasa ne, bayan jinya da ya sha tsakanin Disamba zuwa Janairun 2024.
Ya kuma zura ƙwallo a raga bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu a fafatawar.
Everton ta kasa taka rawar gani, wadda ba ta samu damar kai hare-haren da ya kamata ta farke ƙwallon ba.
Haaland ya ci na biyu ne, bayan da ya samu ƙwallo ta hannun Kevin de Bruyne, bai ɓa ta lokaci ba ya buga ya faɗa raga.
Man City ta haye kan teburin Premier League a karon farko tun bayan 24 ga watan Nuwambar 2023.
To sai dai da zarar Liverpool ta yi nasara a kan Burnley ranar Asabar, za ta koma jan ragamar teburin.
Wannan shi ne wasa na 10 a jere da City ta yi nasara a dukkan fafatawa har da karawar Fifa Club World Cup da FA Cup, sannan na shida a jere a Premier League.
Ita kuwa Everton ta yi kasa cikin ƴan ukun karshen teburin Premier League, wadda ta yi wasa na bakwai ba tare da nasara ba a babbar gasar tamaula ta Ingila.












