Langa: Wasan gargajiyar da ke siffanta yaƙi da jarumta

- Marubuci, Emmanuel Akindubuwa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Akwai wasanni masu yawa da ake gudanarwa a faɗin duniya domin nishaɗantarwa da motsa jiki da kuma fito da al'adu.
Yayin da wasannin kwallon ƙafa da na kwando da zari-ruga suka yi fice a duniya, akwai kuma wasu nau'ukan wasannin gargajiya da ke bayyana al'adun wasu ƙabilu.
Ɗaya daga cikinsu shi ne wasan Langa, wani nau'in wasan gargajiya da ake gwada ƙarfi da ya samo asali daga arewacin Najeriya.
Langa wasa ne da ke nuna juriya da ƙwazo da kuma tunani mai zurfi.
"Al'ummar Hausawa na yi wa langa kallon wasan masu ƙarfi, kuma jarumai,'' kamar yadda Khalid Hussein, shugaban ƙungiyar masu wasan Langa ta jihar Kano ya shaida wa sashen wasanni na BBC.
''Hanya ce da ake iya gane jaruman da za su iya yaƙi da waɗanda za su iya riƙe wanj matsayi a cikin al'umma'' a cewarsa.
Langa wasa ne da ake yi a filin Allah, da ake yi tsakanin bangarori biyu, masu 'yan wasa daga uku-uku zuwa shida-shida, wanda kuma ke buƙatar ƙarfi da juriya da kuma dabara.
Babban abin da ake buƙata a wasan shi ne iya gudu da murƙushe abokin hamayya ta hanyar amfani da hannu ɗaya da ƙafa guda. Sharuɗɗan wasan ya bambanta daga wuri zuwa wuri da kuma nau'in wasan da ake yi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasa ne da galibi ake riƙe ƙafa ɗaya da hannu ɗaya, inda ƙafa ɗaya ke taka ƙasa, kuma da ita zai motsa ko ya yi gudu, sannan da hannu ɗaya zai yi kokawa da abokin hammaya
Kamar yadda wasan yake duk wanda ya taɓa ƙasa ta ƙafar da ya riƙe ko ya faɗi nan take kuma ya fita daga wasan.
An gudanar da wasan ta hanayr tsere ko kokawa domin kayar da abokin hamayya, yayin da ake tantance zakaru galibi bayan an ɗora musu maki 12.
A yayin tsere, kowane ɓangare na da ɗan wasan da ake kira ruwa - wanda galibi akan zaɓi wanda ya ƙware a tsere - wanda zai yi yunƙurin kai wa wani wuri da aka tanada a bayan abokan hamayya.
Ruwa kan ɗauri wani kambi, kuma akan samu wasu jaruman da za su riƙa ba shi kariya, da ake kira 'dawakan ruwa', waɗanda za su yi koƙarin hana abokan hamayya kai wa 'ruwa' farmaki.
A lokacin wasan, yan wasa za su ta ƙoƙarin kayan da abokan hamayyarsu ta hanyar amfani da hannunsu guda yayin da suke tsaye a kan ƙafarsu guda.
Ana kare wasan ne da zarar an kammala kayar da 'yan gida guda, koda kuwa mutum guda ne ya rage a ɓangaren da suka yi kayen, ko kuma idan shi ''ruwa'' ya isa wurin da ake ƙoƙarin hana shi kaiwa.
Wasan ya zarce na wasu mutane

Yayin da ake ganin wasan ya shiga cikin al'adun Najeriya, kyautata zaton cewa wasan ya samo asali daga Najeriya, dabarun gudanar da wasan, kokawa da tsere da jarumta, sun dace da sauran dabarun jaruntar Malam Bahaushe.
A ganin Jamilu Lawan, wani ƙwararren wasan, Langa ya zarta wasan al'ada a wajensa.
"Na fara wasan tun ina ɗan ƙarami. Kuma a yanzu wasan ya zame mini sana'a,'' kamar yadda ya shaida wa sashen wasanni na BBC Afirka.
"Ba fice kawai na yia a wasan ba, har kyaututtuka masu yawa na samu. Na samu kudi a Langa na kuma samu abubuwa masu yawa a rayuwa.''
Wasan Langa na taimakawa wajen motsa jiki da ƙara lafiyar jiki da rage matsalolin ƙwaƙwalwa.
"Langa na da maruƙar muhimmanci a rayuwata, saboda yana ƙara min ƙarfi da lafiya,'' in ji Ibrahim Usman, wani mai wasan Langa.
Bayan kasancewarsa wasa na gasa, Langa na taimakawa wajen haɓaka ɗabi'ar aiki tare da biyayya da juriya.
A cewar Mu'azzam Ibrahim, wanda ke horas da 'yan wasan Langa a jihohin Rivers da Delta da ke kudancin Najeriya, wasan na taimakawa wajen haɓaka ci gaban al'umma da inganta zamantakewa.
"Haƙiƙa, langa na koyar da abubuwa da dama kamar abokata, da mu'amala da ilimi,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.
"Muna damuwa da matsalolin juna, kama da wuraren horo da mu'amalarmu a gida ko a waje, muna ɗaukar kanmu a matsayin 'yan'uwan juna''.
Wasan na samun karɓuwa

Langa ya fara samun karɓuwa a wasu wuraren da a baya aka san shi, kuma ya fara shiga cikin bukukuwan wasannan na Najeriya a 1996
Shugaban ƙungiyar masu wasan Langa Hussein ya ce yana fatan wasan ya kai matakin da ba a tsammata ba.
"Muna fatan ganin langa ya shiga jerin wasannin yammacin Afirka, da kuma gasannin nahiyar Turai,'' in ji shi.
Saukin wasan zai sa a iya shigar da shi cikin wasannin makarantu a duniya, kamar wasu wassanni, langa ba ya buƙatar sayen kayan aiki masu tsada, kawai abin da yake buƙata shi ne kwarewa.
Yayin da wasannin zamani suka mamaye fagen nishaɗi a duniya, wasannin gargajiya kamar langa na fuskantar ƙalubalen kasancewa da muhimmanci.
To sai dai masana na ganin cewa ta hanyar adana tarihi da ƙoƙarin kafofin yaɗa labarai, akwai fatan cewa langa zai samu gurbi a fagen wasannin duniya kamar yadda sauran wasannin gargajiya a faɗin duniya irin su capoeira (na Brazil) da kabaddi (na Kudancin Asia), da kuma sepak takraw (na kudu maso gabashin Asia) suka samu yi fice a duniya.
"Langa ba wai gasa ce kawai ba," in ji Hussein.
"Abu ne al'ada da tarihi da kuma yanki."
Yayin da a yanzu wasan ke ci gaba da samun karɓuwa, langa na da damar shiga jerin manyan wasannin duniya, musamman la'akari da yadda ake aiwatar da shi.











