'Ina fata mala'iku su raka mahaifiyata da bege zuwa makwancinta'
An wallafa
A jawabinsa na alhini da ta'aziyyar rashin mahaifiyarsa, sabon Sarkin Birtaniya Charles na uku ya yi addu'a cikin nuna kauna.
Sarkin ya ce: "Muna fata sahun mala'iku su raka ki da bege zuwa makwancinki."
Ya kara da gode wa mahaifiyar tasa bisa dawainiya da jagorancin da ya ce ta yi wa ahalinta, yana mai cewa "lokaci ya yi da za ki je ki hadu da babana, abin kaunata."








