Man City za ta sake ɗaukar Gundogan daga Barcelona

Gundogan

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City tana kokarin sake ɗaukar Ilkay Gundogan daga Barcelona.

Mai shekara 33 ya bar Etihad zuwa Barcelona a 2023, bayan da kwantiraginsa ya kare, wanda shi ne ƙyaftin lokacin da ƙungiyar ta lashe kofi uku a tarihi.

Ƙungiyar da ke buga La Liga na fama da matsin tantalin arziki, wadda ta kasa kammala cinikin Dani Olmo daga RB Leipzig da ta ɗauka a bana - hakan ya sa za ta rabu da ɗaya daga cikin masu karɓar albashi da yawa.

City ta sayar da Julian Alvarez ga Atletico Madrid kan £81m a bana, sannan Oscar Bobb zai yi jinyar wata huɗu, kenan Gundogan yana da rawar da zai taka.

Tun farko Pep Guardiola bai so Gundogan ya bar City ba a karshen kakar bara, amma yanzu ƙungiyar a shirye take ta sake ɗaukar ɗan wasan.

Bayan da ya koma City daga Borussia Dortmund kan £20m a 2016, Gundogan ya buga wasa 304 da cin ƙwallo 60.

A kaka bakwai da ya yi a Etihad ya lashe kofi 14 daga ciki Premier League biyar da Champions League da FA Cup biyu da Carabao huɗu.

Haka kuma ya ɗauki Community Shields biyu.