Rodrygo ya buga wa Real Madrid wasa na 150 a La Liga

Rodrygo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid ta je ta tashi 1-1 da Atletico Madrid a wasan mako na takwas a La Liga ranar Lahadi.

Rodrygo ya buga karawar, kuma wasa na 150 da ɗan ƙwallon tawagar Brazil ya yiwa Real kuma a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Ɗan wasan na buga kaka ta shida kenan a Santiago Bernabeu, tu bayan da ya fara taka leda, mai wasa 226 a dukkan fafatawa da ya yi.

Kawo yanzu Rodrygo ya lashe La Liga uku a 2019/20 da 2021/22 da kuma 2023/24, an kuma yi nasara 102 da shi a La Liga, ya ci ƙwallo 29 a gasar.

Ƙungiyar da ya fi fuskanta ita ce Real Betis da Real Sociedad da kuma Athletic Club, kowacce ya haɗu da ita sau tara.

Bayan da aka tashi 1-1 tsakanin Atletico da Real, ƙungiyar Barnabeu ta ci gaba da zama ta biyu a kan teburin La Liga da maki 18 da tazarar maki uku tsakani da Barcelona mai jan ragama.

Atletico tana mataki na ukun teburi da maki 16, bayan nasara huɗu da canjaras uku aka doke ta wasa ɗaya daga karawa takwas a gasar ta La Liga.

Ranar Laraba 2 ga watan Oktoba, Atletico za ta je Benfica, domin buga Champions League, sannan ta ziyarci Real Sociedad a wasan La Liga ranar Lahadi 6 ga watan Oktoba.

Ita kuwa Real Madrid za ta kara da Lille a Champions League a Faransa ranar Laraba 2 ga watan Oktoba, daga nan ta kece raini da Villareal a La Liga ranar Asabar 5 ga watan Oktoba a Santiago Bernabeu.